Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Bankin Lotus ya shiga tsaka mai wuya bisa fuskantar binciken ƙwararru daga Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC) bisa zargin cewa an yi amfani da bayanan sirri na wasu ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba wajen buɗe musu asusun banki ba tare da ingantaccen tushe na doka ba.
Hukumar ta kuma fara bincike kan Jami’ar Legas (UNILAG) da kamfanin Hackerbella Ltd, domin gano irin rawar da kowannensu ya taka wajen tattarawa, amfani da su, bayyana wa wasu ko sarrafa bayanan sirrin ɗaliban da lamarin ya shafa.
Shugaban Sashen Shari’a, Tilasta Bin Doka da ƙa’idoji na NDPC, Babatunde Bamigboye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja. Ya ce, binciken ya samo asali ne daga koke-koken jama’a kan zargin cewa an yi amfani da bayanan sirrin ɗalibai wajen buɗe asusun banki ba tare da wani sahihin dalilin doka ba.
Bamigboye ya ce Kwamishinan ƙasa na NDPC, Vincent Olatunji, ya umurci tawagar binciken da ta gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin yadda aka tattara, aka yi amfani da kuma aka raba bayanan ɗaliban.
Ya ƙara da cewa, binciken zai kuma tantance rawar da UNILAG, Lotus Bank da Hackerbella Ltd suka taka wajen sarrafa bayanan da ake magana a kai. A cewar Bamigboye, binciken zai tantance ko waɗannan hukumomi da kamfanoni sun cika nauyin da Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya ta 2023 ta ɗora musu.
Ya ce, binciken zai shafi batutuwa da suka haɗa da gudanar da Binciken Tasirin Kare Bayanai (DPIA), sahihancin doka da bayyana gaskiya wajen tantance cancantar samun bashi ko ƙirƙirar bayanan martabar abokan ciniki, da kuma amfani da tsarin kwamfuta wajen yanke shawara kai tsaye.
Haka kuma, za a binciki isasshiyar sanarwar sirri da aka bai wa masu bayanan, yarjejeniyoyin musayar bayanai, dalilin doka na sarrafa bayanan, rage tattara bayanan da ba su da muhimmanci, iyakance amfani da bayanan ga manufar da aka tattara su, tsawon lokacin adana bayanan da kuma matakan fasaha da na gudanarwa da aka ɗauka domin kare haƙƙin masu bayanan.
Hukumar ta ce za ta kuma duba irin haɗarin da lamarin zai iya haifarwa ga haƙƙoƙi da ’yancin ɗaliban da bayanansu suka shiga cikin wannan batu. Bamigboye ya jaddada cewa cibiyoyin da aka damƙa wa bayanan sirrin ɗalibai, ma’aikata da sauran mambobin al’ummarsu suna da alhakin tabbatar da cewa ana sarrafa bayanan cikin doka, adalci, gaskiya da tsaro.
Ya kuma gargaɗi cibiyoyin ilimi da har yanzu ba su bi umarnin da NDPC ta gindaya kan kare bayanai ba da su gaggauta yin hakan. Ya ce, bin ƙa’idojin kare bayanai na da matuƙar muhimmanci wajen kare haƙƙoƙi da ’yancin masu bayanai, tare da inganta tsarin gudanar da bayanai cikin gaskiya da alhaki a fannin ilimi.
