Bashin tiriliyan N4 na lantarki: Shugaba Tinubu zai gana da Discos

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu zai gana da jagororin kamfanonin raba wutar lantarki a ƙoƙarinsa na warware matsalolin bashin Naira tiriliyan 4 da ke haddasa tsaiko ga hanyoyin raba wuta a Nijeriya.

Hakan ya biyo bayan zama da aka yi tsakanin Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu da jagororin kamfanonin a ranar Talata, a yayin da ake fargabar sake lalacewar rumbun lantarki na ƙasa saboda tsaikon da ke ɓangaren, kamar yadda ma’aikatar lantarki ta bayyana a ranar Lahadi a wata takarda.

Gwamanti ta yi alƙawarin rage bashin tiriliyan N4 da kamfanonin suke bi, bayan da suka yi mata gargaɗi kan ƙalubalen da ka iya samun ayyukansu.

Kamfanonin sun ce, suna bin Naira tiriliyan 2 na raba wuta da kuma tiriliyan N1.9 na wasu haƙƙoƙi da ba a ba su ba.

A sanarwar da Bolaji Tunji, jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ya fitar, gwamanti ta ce za ta biya wani kaso na kuɗin kana daga bisani cikin watanni shida ta biya sauran ta hanyoyi da suka dace.

Ya kuma ce, gwamnati ta yi hakan ne don kare sake faruwar katsewar lantarki a ƙasar kasancewar matsala ce ta gaggawa ga ƙasar da al’ummarta.

By Babaji