Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da wani shahararren ɗan TikTok ya rasu.
Shahararren ɗan TikTok ɗin mai suna ‘Disturbing’ ya mutu ne yana tsaka da naɗar bidiyo kai tsaye.
‘Yar jarida mai bincike, Temilola Sobola, ita ta tabbatar da labarin a shafinta na Instagram inda ta wallafa faifan bidiyon.
A bidiyon, an gano lokacin da ɗan TikTok din ya fara shiɗewa har ya mutu yana cikin yin shirin kai tsaye.
A lokacin da aka kawo rahoton, babu wata sanarwa daga hukumomi da ta tabbatar da ainihin dalilin rasuwar Disturbing.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ba a yi wata-wata ba bayan rasuwar marigayin an yi sallar jana’izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada.
Wannan al’amari mai tayar da hankali ya karaɗe kafafen sada zumunta inda aka nuna lokacin da ya fara rawar jiki kafin ya faɗi ya mutu.
Disturbing ya shahara ne saboda goyon bayansa ga neman adalci ga mawaki Mohbad da ke zargin an kashe.
Wasu mutane sun ce ya kasance yana zagin mahaifiyar Mohbad, matarsa, ɗan uwansa Adura da Liam yayin da yake watsa shirye-shiryen kai tsaye.
Wasu masu amfani da kafofin sadarwa sun bayyana cewa mutuwar na da nasaba da amfani da miyagun ƙwayoyi da ya daɗe yana yi.
Mutane da dama sun yi martani kan tashin hankalin da suka gani a bidiyon, suke yi masa fatan samun rahama.
Duk da haka, wasu sun nuna damuwa kan yadda yake zagin iyalan marigayi Mohbad a cikin bidiyonsa a ƙoƙarin neman adalci ga matashin mawakin da ake zargin kashe shi aka yi.
