Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Laraba ya musanta naɗa wanda ake zargin ɗan ta’adda ne kuma ɗan bindiga, Bashir Hadejia, a matsayin mataimaki na musamman a gwamnatinsa.
An kama Hadejia ne a ranar Litinin ɗin makon jiya bisa zargin cin amanar ƙasa da zagon ƙasa ga jihar.
Wanda ake zargin dai shi ne mai ba wa Aaramin Ministan Tsaro na ƙasa, Bello Matawalle shawara na musamman a lokacin yana Gwamnan Jihar Zamfara.
Bayan kama shi, wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 27 ga Oktoba, 2023, wacce aka ce sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Mal Abubakar M. Nakwada, ya sanya wa hannu, ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta bayar da wani muƙami ga wanda ake zargin ɗan bindigar ne ya yi ta zagayawa a yanar gizo.
Sai dai da yake magana a wata hira da gidan Talabijin na Channels Television’s Politics Today, gwamnan ya ce wasiƙar naɗin da aka yi zargin ƙarya ce.
“Bari in yi wata magana ta musamman a nan. Ban naɗa Hadejia a matsayin mataimaki na musamman ba,” inji gwamnan.
“Idan ka kalli wasiƙar kan kanta da kwanan watan, akwai shubuha a ciki. Mun fitar da sanarwar cewa babu ruwan mu da wannan, takardan jabu ne.
“A duk lokacin da na naɗa masu ba da shawara, na kan gaya wa kafafen yaɗa labarai cewa na naɗa wane-wane a muƙamai daban-daban. Ina ƙalubalantar kowa da ya nuna min inda muka yi irin wannan magana a kan Hadejia.”
Ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa babu wani abin ɓoyewa.
A yayin bikin, gwamnan ya kuma yi tsokaci kan ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar arewa maso yamma.
A cewarsa, rashin tsaro ya ragu matuƙa domin a yanzu manoma na iya komawa gonakinsu.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta na aiki kafaɗa da kafaɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da Ma’aikatar Tsaro domin amfanin al’ummar Zamfara bakiɗaya.
