Batun yunƙurin juyin mulki ba gaskiya ba ne, inji Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce jita-jitar juyin mulki da wasu kafafen yaɗa labarai suke ruwaitowa ba gaskiya ba ne.

A wata sanarwar da Kakakin DHQ, Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo ne suka ruwaito batun ta hanyar kafa hujja da soke faretin soji na bikin Ranar ‘Yancin Kai, da kuma wasu jami’an rundunar da ake bincika da zargin karya ƙa’idar aiki.

“Rundunar sojin Nijeriya na tabbatar da cewa rahoton na ƙarya ne baki ɗayansa,” a cewarsa. “An dakatar da faretin Ranar ‘Yanci ne saboda a bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani taro a wajen Najeriya, da kuma mayar da hankali wajen yaƙi da ta’addanci da ƴan fashin daji.

“Binciken da ake yi wa jami’ai 16 kuma na yau da kullum ne da aka saba domin tabbatar da ɗa’a da ƙwarewar aiki. An kafa kwamatin bincike kuma za a sanar da sakamakon bincikensa.”

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da faretin soji na al’ada da aka saba yi duk ranar bikin ‘yancin kai na ranar 1 ga watan Oktoba ba tare da wani takamaiman dalili ba.

Bayan bikin ne kuma rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar 4 ga watan Oktoba cewa ta tsare jami’anta 16 bisa laifuka daban-daban da suka shafi rashin da’a da kuma karya ƙa’idar aiki.

By Babaji