
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzu mutum 17 ne suka rasu bayan arangama tsakanin ƴan bindiga da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Da fari wasu rahotannin sun ce mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, inda a yanzu adadin ya kai 17, kamar yadda AFP ta ruwaito.
A ranar Alhamis aka yi fito na fito tsakanin ɓangarorin biyu a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, inda ake fama da matsalolin ƴan bindiga da masu haƙar ma’adinai ta haramtattun hanyoyi.
A cewar wani rahoton tsaro daga AFP, rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani sanannen ɗan bindiga ya ƙwace gwal a hannun wasu ƴan haƙar ma’adinai a ɗaya daga cikin haramtattun wuraren haƙar ma’adinai a yankin.
Akan haka ne ƴan haƙar ma’adinan suka haɗa kai inda suka farmaki ƴan bindigan tare da halaka sanannen ɗan bindigar a nan take.
A yayin martani, dabar mamacin suka koma wajen haƙar ma’adinan inda suka ta yin harbe-harbe tare da halaka mutane bakwai.
Daga nan ne faɗan ya faɗaɗa zuwa wani ƙauye mai suna Layin Ɗan-Auta inda a nan ma aka halaka mutane tara da raunata wasu 13. Haka kuma an yi garkuwa da wasu da dama da kuma lalata gidaje da dukiyoyi masu yawa.
