Ƙalubalen kafa ’yan sandan jihohi ga magance rikice-rikice

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

An fara muhawarar samar da ’yan sandan jihohi a ƙasar nan, kimanin shekaru 20 ko fiye da haka, sakamakon ƙalubalen tsaro da aka riƙa fuskanta a wasu jihohi, musamman a Jihar Filato. Tun da aka fara samun rikicin addini da ƙabilanci a Jihar Filato a shekarar 2001, batun samar da ’yan sandan jihohi ya fara bayyana. Saboda barazanar da gwamnoni a lokacin suka fara samu ta rashin samun ƙarfin iko kan ’yan sanda da jami’an soja, game da yadda za a bi tsarin da suke so wajen kama masu laifi ko waɗanda ake zargi da haddasa rikici ko tarzoma. A dalilin yadda aka lura gwamnonin na shigar da siyasa da son zuciya cikin harkokin tsaro.

Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu  ana cigaba da muhawara akan wannan batu, sakamakon yadda baki ya rabu kan tsoron da ake da shi, idan ƙarfin ikon juya al’amarin tsaro ya shiga hannun ‘yan siyasa ko gwamnoni. Sai dai kawo yanzu da alamu an kusa kawo maƙura, domin kuwa kusan dukkan gwamnonin ƙasar nan sun gabatar da buƙatar samar da ‘yan sandan jihohi, ta yadda za su samu damar ɗaukar matakai kan al’amarin tsaro a jihohin su ba tare da katsalandan ɗin Gwamnatin Tarayya ba. 

Rahotanni sun bayyana cewa, ko a taron baya bayan nan da gwamnonin Arewa 19 da suka gudanar a Kaduna, majalisar gwamnonin ta bayyana buƙatar samar da rundunar ‘yan sanda mallakar jihohin Borno, Binuwai, Filato, Katsina, da Zamfara, domin a samu damar ɗaukar matakan da suka kamata wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihohin nasu. Sakamakon yadda ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai suke cin karensu babu babba, suna kai hare-hare kan ƙauyuka da gonaki, suna haifar da ɓarnar rayuka da dukiyoyi.

Sai dai har kawo yanzu a ɓangaren Gwamnatin Tarayya batun na fuskantar cikas sakamakon rashin samun goyon bayan da ake buƙata. Rahotanni na bayyana cewa, ko a wajen taron Majalisar Kula Da Tattalin Arziki ta ƙasa da aka gudanar a watan da ya gabata, batun samar da ‘yan sandan jihohi shi ne na ƙarshe a jerin abubuwan da aka tsara za a tattauna a taron. Kuma duk da haka ma ba a samu damar tattaunawa ba, haka aka tashi a taron. 

Masu goyon bayan a kafa ‘yan sandan jihohi na ganin duk wani laifi da ake aikatawa ana yin sa ne a cikin ƙauyuka da yankunan da ke ƙarƙashin ikon jihohi, amma kuma gwamnoni ba su da ikon tafiyar da harkokin tsaron yankunan yadda ya kamata, ɗari bisa ɗari. Alhalin a cewar su, a lokacin Jamhuriya ta Farko, kowanne lardi shi yake da hurumin tafiyar da harkokin tsaro a yankinsa.

Wani ƙarin matsalar da ake fuskanta a game da batun tsaro a jihohi shi ne rashin wadatar jami’an ‘yan sandan, sakamakon yadda a kullum adadin ‘yan sandan da ake da su ke raguwa, saboda barin aiki da mutuwa da suke yi, ba tare da ana cike guraben da suke bari ba. Bincike ya nuna adadin ‘yan sandan da ake da su a ƙasar nan ba su wuce dubu 400 ba. Wanda hakan ke nuna, kowanne ɗan sanda ɗaya yana kula da mutum 600 ne, saɓanin yadda Majalisar ɗinkin Duniya ta buƙaci kada ya wuce mutum 450. Sannan harwayau, ga rashin kayan aiki na zamani ga motocin sintiri ko zuwa kai ɗaukin gaggawa. Wannan ne ya sa wasu jihohin suka fara kafa ƙungiyoyin ‘yan banga da rundunar ‘yan sakai da za su riƙa tallafawa jami’an ‘yan sandan wajen gudanar da ayyukan su na samar da tsaro. Har ma a wasu jihohin, jami’an ‘yan sakai sun fi samun dogaro da zama abin dogaro.

A Jihar Anambra, akwai rundunar Agunechemba da ke aikin samar da tsaro bisa tsari irin na ‘yan banga, wanda gwamnatin jihar ke tallafa musu. Kamar yadda ake da Amotekun a jihohin Yarabawa, ko kuma hukumar rundunar ‘yan sandan shari’a ta Hisbah a wasu jihohin Arewa, irin su Kano, Bauchi, Katsina da sauran su. Ba da jimawa ba ma gwamnatin Jihar Katsina, Gombe, da Zamfara sun kafa wasu rundunonin ‘yan sakai dake taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ‘yan bindiga da ɓata gari da ke fakewa cikin ƙauyuka da unguwanni suna cutar da jama’a. Kodayake, saboda rashin ƙwarewa da samun ingantaccen horon da ya kamata, ana yawan fuskantar kurakurai, musamman wajen ɗaukar matakin wuce gona da iri. 

Ba da jamawa ba, mun ga yadda ‘yan banga a Uromi ta Jihar Edo suka kashe wasu mafarauta 16 ‘yan asalin Jihar Kano da suka fito daga Fatakwal inda suka je farauta. Sannan a Jihar Kano akwai ƙorafe-ƙorafe game da zargin jami’an Hisbah, da wuce gona da iri, wajen gudanar da ayyukan su. Yayin da a jihohin Katsina, Sakkwato, da Zamfara ake zargin ‘yan sakai da yi wa waɗanda ake zargi da kisan gilla ko zaluntar waɗanda ake zargi, ba tare da an gurfanar da su gaban shari’a ba. Sannan ana zargin wasu daga cikin su da haɗa baki da ýan bindiga wajen bayar da bayanai. 

Lallai akwai abin dubawa sosai a al’amarin kafa ‘yan sandan jihohi da ƙungiyoyin sakai ko ‘yan banga. Wani abin tambaya kuma shi ne, batun biyansu alawus ko albashi mai mutunci da ya kamata a riƙa biyansu. Ta yaya jihohi za su iya jurewa su biya su albashin su kowanne wata, a yayin da ma’aikata a jihohinsu ke kukan rashin biyansu albashi mafi ƙaranci. Rashin magunguna a asibitoci, da kula da ilimin makarantun firamare da sakandire da ke ƙarƙashin kulawar su. Yadda wasu gwamnoni da ýan siyasa ke amfani da ‘yan daba ko ’yan bangar siyasa, wajen takura wa abokan adawarsu a siyasance, akwai abin tsoratarwa. A wani jawabi da Babban Sufeton ýan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya gabatar ya yi ƙorafin wasu gwamnoni za su iya amfani da ’yan sandan jihohi don cimma ra’ayin su na siyasa, tauye haƙƙoƙin ɗan adam, da amfani da ƙabilanci ko wani bambanci, da zai iya hassala batun tsaro a jihohin su.

Irin wannan fargabar ce wasu ’yan Nijeriya ke nunawa, bisa la’akari da yanayin siyasar jihohin su ko wani batu na tsaro da yake haifar da matsalolin zamantakewa da siyasa. Kamar abin da ke faruwa a Jihar Filato, inda al’ummar Musulmin jihar suke nuna damuwa da irin bambancin da Gwamna Caleb Mutfwang ke nuna musu, lura da halin taɓarɓarewar tsaro da jihar ke ciki. 

Wata ƙungiya da ta kira kanta da suna ƙungiyar Musulmi ’yan asalin Jihar Filato, ta zargi gwamnan da nuna wariya ga Musulmin jihar, musamman a baya bayan nan, sakamakon ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan jihar. ƙungiyar ta zargin Gwamnan da nuna halin ko-in-kula da kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa wasu ‘yan banga a yankin ƙaramar Hukumar Kanam, inda aka kashe aƙalla ’yan banga 70. Sannan a yankin Kukawa na ƙaramar Hukumar Wase ma ‘yan bindiga sun kashe 8. Amma duk wannan bai sa Gwamnan ya ziyarci yankunan ya nuna alhini da jimaminsa kan abin da ya faru ba, domin ƙara musu ƙwarin gwiwa da jajenta musu. Wannan na zuwa ne bayan da aka ga Gwamnan ya yi gaggawar zuwa inda aka kai wani hari kan wasu al’ummar Berom a ƙauyukan ƙaramar Hukumar Riyom, inda aka kashe mutane 27, a wajen ne kuma har ya nemi Gwamnatin Tarayya ta cire sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin a maye gurbinsu da ’yan sandan kwantar da tarzoma. 

Wannan abin da Gwamnan ya yi ya haifar da cece-kuce a jihar, wacce ke cikin ɗumin fitintinun hare-haren ‘yan bindiga, da zarge-zargen juna. Reshen ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Filato da wata ƙungiyar matasan Musulmin jihar, duk sun fito sun ƙalubalanci wannan furuci na Gwamnan, da suka ce barazana ce ga halin rashin tsaro da jihar ke ciki. Tare da nuna rashin jin daɗi da irin wariyar da ake nunawa musulmi a jihar, musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziki. ƙungiyoyin sun koka da yadda suka ce a cikin shugabannin ofisoshin ’yan sanda (DPO) 39 da ake da su a faɗin jihar guda ɗaya ko biyu ne kawai Musulmi. Sannan a baya lokacin da ake cikin tsakiyar rikicin Jos, an yi amfani da wasu baragurbin ‘yan sandan kwantar da tarzoma wajen kashe mutane aƙalla 700 a rana ɗaya, cikin shekarar 2008.

Waɗannan batutuwa sun ƙara tayar da ayar tambaya kan, anya kuwa gwamnonin jihohi za su iya tafiyar da harkokin tsaro a jihohin su ba tare da sun ci zarafin wasu ko tauyen haƙƙoƙin wasu, bisa bambancin addini ko siyasa ba? Wanne sauyi za a iya samu a waɗannan jihohi, fiye da wanda ake samu ƙarƙashin rundunar ’yan sanda ta Gwamnatin Tarayya da sauran rundunonin tsaro da ake da su a ƙasar nan?

By ukarofi