Bauchi ta ƙaddamar sabuwar kotun bin ba’asin haƙƙoƙin jama’a

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Babbar mai Shari’a ta jiha, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar a makon daya gabata ne ta ƙaddamar da wata sabuwar ƙaramar kotu mai bin ba’asin ƙananan haƙƙoƙin jama’a, musamman waɗanda suka jiɓanci bashin kadarori ko kuɗaɗe ko majiɓantan lamuran kasuwanci.

Wannan sabuwar kotun bin ba’asin haƙƙoƙin jama’a tana da rassa guda uku, guda biyu a shiyyar Bauchi, guda a shiyyar Katagum, waɗanda Alƙalan lardi (Majisri) za su jagoranta da suka haɗa da Alkali Abdullahi Garba, Alkali Kawu Bala da Alkaliya Zainab Shu’aibu.

Da take ƙaddamar da sabuwar ƙaramar kotun, Babbar mai Shari’a ta jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ta bayyana cewar, kafa wannan kotu wata hanya ce ta sauƙaƙa gudanar da shari’a cikin gaggawa akan batutuwa da suka jiɓanci ma’amala ko bashin kuɗaɗe da ba su haura kuɗi Naira miliyan uku ba.

Mai Shari’a Rabi Umar ta ce ɓangaren shari’a na gwamnatin jihar Bauchi ya bijiro da wannan tallafi ne wa al’ummar jiha ta hanyar kafa wannan sabuwar kotu mai bin ba’asin haƙƙoƙin jama’a, wanda cimma nasarorin gudanar da ayyukanta ya ta’allaƙa ne kwacakwam bisa jajircewar wani kwamitin sharia dake ƙarƙashin jagorancin Mai Sharia Mua’zu Abubakar.

Rabi ta bayar da tabbacin cewar, wannan tallafi na fuskar shari’a da sannu zai inganta matuƙa gaya ta yadda za a ci gajiyar amfanin sa akowane sashi da lungu na ɗaukacin ƙananan hukumomi ashirin dake cikin jihar Bauchi, tana mai cewa, tuni kwamitin shari’ar ya tura illahirin ma’aikata da suka dace wa sassa daban-daban na kotunan guda uku da tuntuni suka fara zama a garuruwan Bauchi da Azare.

Babbar Mai Shari’a Rabi ta ƙara da cewar, a halin yanzu an samar wa babban kotun jiha ɗinkakkar kafar yanar gizo, haɗu da mawaka mahanga ta wannan sabuwar kotu mai bin ba’asin haƙƙoƙi a farfajiyar yanar gizon domin amfanin jama’a.

“Za a wadata shafin maganar da bayanai na tarihi dangane da wannan ƙaramar sabuwar kotu, haɗi kofe-kofe na irin yadda take gudanar da ayyukan ta kan adireshi mai lamba biyu cikin wani sahihin littafi, matsugunar kowace kotu, suna da muqamin kowane alƙali, rahoton tsarin gudanar da ayyuka, kofe more na ire-iren shari’u da aka zartar, haɗu da majivancin bayanai da kwamitin shari’a za ta ke bayarwa a loto-loto.

Mai Shari’a Rabi Umar ta ce, “an buga dukkan kowanne ire-iren takardun gudanar da ayyuka da kotunan ke buƙata, kamar takardar buqatar biyan kuɗaɗe, takardar bin haƙƙoƙi, takardar yin sammaci, rantsuwar rashin isar da sammaci, neman kariya ko akasi don bin haƙƙi, rantsuwar isar da sammaci, ƙuduri don yanke hukunci, da takardar ƙudurin ɗaukaka ƙara. Ina mai baku tabbacin cewa mun shirya tsaf, kamar yadda a yanzu haka nake ƙaddamar da wannan sabuwar kotu mai bin ba’asin hakkokin jama’a ta jihar Bauchi a wannan rana ta 11 ga watan Mayu na shekarar 2023.”

Da yake yin marhabun wa manyan baƙi da suka halarci bikin ƙaddamar da sabuwar kotun tunda farko, babban magatakardan babbar kotu ta jihar Bauchi, Barista Subilim Emmanuel Ɗanjuma ya bayyana cewar, kafa wannan sabuwar kotu wani tallafi ne ta fuskar Shari’a data biyo kyakkyawan salon tsarin gudanar wa na bai ɗaya na duniyar mu ta yau na sauƙaƙa bin ba’asi akan jinga, kwantaragi, yarje-jeniya ko alƙawari dangane ko kan ƙanana ko matsakaitan sana’o’i a gaban masu shari’a.

Barista Subilim Ɗanjuma ya bayyana cewar, laramar kotun bin ba’asin hakkoki, wata kotu ce ta musamman dake gudanar da ayyukan ta cikin gaggawa da aka kafa bisa tsarin gudanar da ayyukan kotunan lardi (Magistrates) da zumar samar wa maƙarayi ko maƙarƙashiya hanya mafi sauƙi wajen bin ba’asin haƙƙoƙin bashin kuɗaɗe da suka yi nauyin biya.