Bayan dakatarwa, DSS ta gayyaci tsohon limamin masallacin Sahaba, Bin Uthman

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar gudanarwa ta Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da ake kira Masjid Sahaba, ta dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar sallah da huduba bayan wata huɗubar da ya yi mai cike da cece-kuce a ranar 24 ga Janairu.

Sheikh Uthman, wanda ya shugabanci tsohon masallacin fiye da shekaru 24, ya koka a huɗubarsa cewa an ware shi daga shugabancin sabon masallacin, inda kwamitin masallacin ya naɗa wasu limamai uku ba tare da naɗashi babban limami ba. Wannan magana ta tada hankalin masu ibada, inda wasu suka yi yunƙurin afka wa sakataren kwamitin masallacin, Abdulkadir Isawa.

Biyo bayan wannan rikici, kwamitin masallacin ya fitar da takarda mai ɗauke da sa hannun daraktan gudanarwa, inda aka dakatar da Sheikh Uthman ba tare da wa’adi ba. Haka kuma an buƙace shi da ya miƙa duk wasu kayayyakin masallacin da ke hannunsa. Hukumar tsaro ta DSS da Majalisar Malamai sun kira Sheikh Uthman da kuma AY Maikifi, wanda aka ware filin masallacin gareshi, domin tattauna lamarin.

Bisa bayanai daga DSS, an gargaɗi Sheikh Uthman da gujewa kalaman da ka iya haifar da rikici ko tashin hankali a cikin masallacin. A nasa ɓangaren, Majalisar Malamai ta shawarce shi da komawa tsohon masallacinsa. Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko zai amince da wannan shawara ba.

By ukarofi