
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake cigaba da karawa a gasar Olympics ɓangaren ƙwallon ƙafa, ƙasar Sifaniya ta doke mai masauƙin baƙi, Faransa a zango na ƙarin lokaci na wasan ƙarshe.
Hakan na zuwa ne bayan da Sifaniya ta yi nasara da ci 5-3 wanda hakan ya sanya ta samun kyautar gwal a gasar a matsayinta ta ɗaya.
Faransa itace ta fara zura ƙwallo a minti na 11 inda ba tare da ɓata lokaci ba, Sifaniya ta mayar da wasan kunnen doki. Daga baya ne su ka yi ta bayayyar zura ƙwallo a tsakanin su da har ta kai su ga zangon ƙarin mintuna 30 a lokacin da ake 3-3 wanda kafin a ƙarƙare wasan ne Sifaniya ta samu damar zura ƙwallaye biyu
Wannan shi ne karo na biyu da ƙasar ta yi irin nasarar tun a shekarar 1992 da aka gudanar da gasar a Barcelona, babban birnin ƙasar.
