Bayan rubutu Ina faɗakarwa da sasanta tsakanin masoya – Sakina Isma’il

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

MANHAJA: Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu akai, kuma wanne lokaci ne ki ka fi jin daɗin yin rubutu?

SAKINA ISMA’IL: Ta hanyar yin tunani da nazari kan al’amuran da ke faruwa a inda nake, sai in zauna in tsara labarin cikin basirar da Allah ya bani. 

Wanne alheri ki ka taɓa samu a dalilin rubutu?

Gaskiya babu wani abu da na taɓa samu muhimmi daga rubutun da nake yi, sai arziƙin jama’a da masoya da kullum suke sa min albarka da addu’o’in fatan alheri, bisa yadda suke amfana da rubutun da nake yi. Alhamdulillah. 

Yaya ki ke sanin labarinki yana samun karɓuwa a wajen masu karatu?

Ta hanyar yin sharhi da suke yi, ko kuma in ban yi ba kwana biyu, suna nemana su tambaye ni ko lafiya? Sannan idan littafin da nake yi na kuɗi ne, shi ma ina gane yana karɓuwa ne daga yadda ake tambaya ana saya.

Ta yaya ki ke mu’amala da masu bibiyar littattafan ki?

Muna da kyakkyawar mu’amala da su sosai, saboda ina da saurin sabo, a rana ɗaya ma zamu haɗu na nuna kamar na daɗe da haɗuwa da kai. Tsakanin mu da su sai sambarka! 

Bayan rubutu akwai wata harka da ki ke yi ne, ta sana’a ko kasuwanci?

E, ina da sana’a da nake yi ta sayar da turare. Sai kuma faɗakarwa da nake yi da sasanta tsakanin masoya da ma’aurata. 

Ba mu labarin zauren ki wato Channel ɗin ki na WhatsApp, wanda ki ke faɗakar da mata?

Na buɗe Channel ne da farko saboda tura littattafaina, daga baya kuma sai na yanke shawarar fara faɗakar da matan aure da suke samun matsala a gidajen aurensu, daga haka ‘yammata ma suka ɗinga bina ta bayan fage suna min ƙorafi akan samarin su, basa son su ko kuma baya kulawa da su, gashi nan dai kala -kala. Wannan faɗakarwa da nake yi ba ƙaramin jin daɗinta da farin ciki nake yi ba, saboda godiya suke yi min.

Wanne tasiri abubuwan da ki ke faɗakarwa akai suke yi a rayuwar mata, musamman ta fuskar zamantakewar aure?

Suna jin daɗi sosai saboda yadda faɗakarwar ke tasiri a rayuwarsu, tunda da kansu suke bina suna neman shawara. Wani lokaci idan na yaɗa rubuce-rubucen da nake yi a wasu zaurukan sai wata ta bi ni ta ce wallahi kamar rayuwarta sak, don haka take fuskanta a gidan mijina. 

Wanne ƙalubale ne ki ke ganin ya fi damun mata a wannan lokaci, wanda ya kamata su gyara?

Gaskiya akan ‘yammata kullum nake magana, ‘yammatan da suke bada kansu a wajen maza, saboda son abin duniya, shi ya fi damuna. Don a gaskiya wannan abin yana bani haushi sosai. Suna mantawa da cewa in har suka bai wa namiji jikinsu shi kenan sun yi sallama da budurcin su, ba za su sake komawa yadda suke a baya ba. Sannan kuma wannan zunubin yana nan yana bin su haka za su mutu su koma ga Allah, ranar alƙiyama a tashe su a tambayesu abin da suka aikata. Haƙiƙa idan na duba wannan abin yana ɗaga min hankali sosai, kuma shi ne ya sa nake yin iya bakin ƙoƙarina don ganin cewa su ma sun gyaru sun tuba sun koma ga Allah. 

Idan kin samu dama wanne gyara za ki so ki kawo don cigaban rayuwar mata da marubuta ýan’uwanki?

Gyaran da zan so in yi shi ne akan masu rubutun batsa, don kawai samun kuɗi, sun manta cewa ta dalilin irin waɗannan littattafan ‘yam mata da da yawa suna lalacewa. Don haka gyarana ta kansu zai fara, a lokaci guda kuma ina kira ga dukkan marubuta da mu gyara tare da tsarkake alƙalaminmu, domin samun tsira ranar gobe ƙiyama. 

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a rayuwarki?

Ina da burin na zama babbar marubuciya sosai, na fi yadda nake a yanzu. Sannan kuma na zama babbar malama da za ta riƙa gyara wa mata zamantakewar su ta aure.

To, na gode.

Alhamdulillahi. Ni ma ina godiya.

By ukarofi