Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani abin mamaki ya karaɗe shafukan sadarwa bayan da ƴan Nijeriya suka fara tura wa ƴan bindiga lambobin bankunansu sakamakon yabon shahararren ɗan ta’addan nan mai Bello Turji yayin zanga-zangar da ke gudana a Nijeriya.
A ranar 1 ga watan Agusta ne aka fara zanga-zangar wanda daga baya ta sauya salo a wasu yankunan inda aka yi ta satar dukiyar al’umma da ta gwamnati.
Yayin da zanga-zangar ke raguwa a faɗin ƙasar ne, ƴan bindiga suka sanar da batun raba kuɗaɗe don nuna godiyarsu na yabon shugabansu da wasu ƴan ‘TikTok’ ke yi inda suka kira shi da ‘jarumi’ a yankin Arewacin Nijeriya.
Ya ce, “aminci da albarkatu su tabbata a gare ku ƴan Nijeriya. Masu zanga-zanga, mun ji ku na yabon Bello Turji. Mun gode, mun gode da fatan ku yi nasara. Bello Turji ya na gaisuwa. Ku turo lambobin account ɗinku. Bello Turji zai mu ku wani abu.”
Baya ga haka ne, jama’a da dama suka yi ta tura lambobin nasu kamar yadda aka yi ta gani sashen tsokaci (kwament) a wani bidiyo da ya karaɗe kafar sadarwa.
Sai dai, faruwar wannan al’amari ya haifar da cecekuce kan yadda kafar sadarwa ta shiga tsakanin tasirin ƴan ta’adda da kuma fahimtar al’umma a Nijeriya.

