Bello ya koka kan yadda ‘yan siyasa da jami’an gwamnati ke saida wa ‘yan fashi bayanan sirri

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce wasu ‘yan siyasa da na kusa da gwamnati sun zaɓi zama ‘yan leƙen-asiri ga ‘yan bin bindigar da suka addabi jihar saboda kuɗi inda sukan saci bayanan sirri na gwamnati suna kai wa ɓarayin.

Gwamna Bello ya bayyana haka ne a Talatar da ta gabata a lokacin da yake ƙaddamar da rundunar tsaro ta musmman mai jami’ai 161 domin yaƙi da rashin ɗa’ar matasa a Minna babban birnin jihar.

A cewarsa, “Akwai ‘yan siyasa da wasu na kusa da gwamnati da ke satar bayanai suna kai wa ɓarayin. Ko da taro muka yi, ba da jimawa ba za a ji ɓarayin suna bayyana abin da gwamnan ya faɗa a wajen taron.”

Ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ke neman yin kuɗi ko ta halin ƙaƙa yayin da aka yi garkuwa da yara ‘yan shekara 3 zuwa 11.

Bello ya ce wasu makusantan gwamnati “Sun ce wai a kawo kuɗi don su je su kuɓutar da yaran ni kuma na tambaye su, ‘A ina za ku ga yaran?”

Kazalika, Bello ya koka kan yadda ake yaɗa labaran harkokin gwamnati wanda a cewarsa ta hakan ‘yan bindigar kan san irin shirin da gwamnati ke yi a kansu.

Ya ce, “Mai yiwuwa ku yi tunanin cewa ɓarayin ba su da ilimi amma kuma suna da basirar tattara bayanai.”

Gwamnan ya bai wa sabuwar  rundunar sabbin motoci guda 10 da babura 20 don yin sintiri a garin Minna don magance matsalar matasan da suka addabi al’umma.

A nasa bangaren, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Adamu Usman, ya bayyana cewa ƙirƙiro wannan runduna ta musamman ya zama wajibi ne domin tabbatar da zaman lafiya a Minna.

Usman ya ci gaba da cewa, yayin da rundunar za ta yi fama da matsalar matasa mara ɗa’a a Minna da kewaye, su kuwa sauran jami’an tsaron jihar za su ci gaba da yaƙi ne da harkokin ‘yan fashin dajin da suka yi wa jihar tarnaƙi.

Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa abubuwan hawan da Gwamna Bello ya ƙaddamar za a yi amfani da su yadda ya kamata domin cimma manufar samar da su.