Bikin Soja na Chana ya nuna ƙarfi da dabarun siyasa a idon duniya

Spread the love

A ranar Laraba 3 ga Satumba, 2025, birnin Beijing ya kasance cike da hoton tarihi yayin da ƙasar Chana ta gudanar da biki mafi girma na soji domin tunawa da cikar shekaru 80 da ƙarewar Yaƙin Duniya na Biyu. Wannan biki ya tara shugabanni da dama daga ƙasashe, ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, abin da ya jawo cece-kuce a duniya baki ɗaya.

Shugaba ɗi Jinping ya yi jawabi mai cike da sakonni, inda ya bayyana cewa duniya na fuskantar zaɓi tsakanin zaman lafiya da yaƙi. A cewarsa, ƙasar Chana za ta ci gaba da kare kanta da kuma abokanta, amma tana fatan samun duniya mai cike da zaman lafiya da adalci.

Bikin tunawa da Yaƙin Duniya na II ya kasance al’ada a Chana tun shekaru da dama, amma wannan na bana ya bambanta saboda karfafa gwiwar soji da aka yi ta hanyar nuna makamai na zamani. An nuna sabbin jiragen yaƙi, makaman nukiliya, da kayan fasahar zamani, abin da ya nuna irin ci gaban sojin ƙasar.

ƙasar Amurka da wasu ƙasashen Turai sun nuna damuwa, suna masu cewa bikin ya kasance wata hanya ta nuna karfi da barazana. Masana sun ce halartar Putin da Kim Jong-un ya nuna yadda ake ƙara samun sabuwar kawance tsakanin ƙasashen da ke kallon yamma a matsayin abokan gaba.

Masu nazarin al’amuran ƙasa da ƙasa sun yi hasashen cewa wannan biki zai ƙara tayar da tunani kan makomar tasirin Chana a duniya, musamman a yankin Asiya. Wani masanin al’amura daga Jami’ar Harvard ya bayyana cewa: “Chana na ƙoƙarin gina sabon tsarin duniya inda ita za ta kasance a gaba, ba wai kawai a fannin tattalin arziki ba, har ma a fannin tsaro da soja.”

By ukarofi