Siyasar Nijeriya cike take da butulci – Jonathan game da rashin nasararsa a 2015

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya magantu kan faɗuwarsa a babban zaɓen 2015, inda ya ce ya fuskanci butulci daga ƴan siyasa kasancewar da dama daga cikinsu basa kiyaye abinda aka yi yarjejeniya da su a kai.

Da yake jawabi a taron cikar tsohon shugaban ma’aikatansa Cif Mike Aiyegbeni Oghiadomhe shekeru 70 a duniya a Benin, babban birnin jihar Edo, Jonathan ya bayyana siyasar Nijeriya a matsayin abinda ba shi da tabbas duba da yadda yaudara da makirci suka yi yawa a cikinta.

Jonathan ya hakaito irin ƙalubalen da ke tattare da haɗakar ƴan siyasa wanda a lokacin ya rasa damar lashe zaɓen, lamarin da a cewarsa ke nuna kalar makomar wa’adin mulkin ƴan siyasa da dama a ƙasar.

A cewarsa, rashin gaskiya tsakanin ƴan siyasa a Nijeriya ya sa yake da wahalar gaske a iya amincewa da wani ɗan siyasa ɗari bisa ɗari.

Saidai duk da haka, tsohon shugaban ƙasar ya tsame Oghiadomhe daga cikin su inda ya ce shi mutum ɗaya ne daga cikin kaɗan da za a iya amince musu acikin sauran.

By Babaji