Binciken badaƙalar Abacha ta $499m: Malami zai riƙa zuwa EFCC kullum a Disamba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ce tsohon Antoni Janar Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), zai rika bayyana a hedikwatarta kowace rana daga ranar 1 zuwa 31 ga Disamba domin cigaba da bincike kan batun dala miliyan 499 na kuɗin Abacha da aka dawo da su ta hanyar Mutual Legal Assistance (MLAT).

Wata majiya daga cikin hukumar ta bayyana cewa an hana Malami fita daga Nijeriya na tsawon wata guda.

Haka kuma an ƙwace fasfo ɗinsa kamar yadda ake yi yayin bincike domin tabbatar da kammala aikin bisa tsari.

Majiyar ta bayyana cewa, “ya na da takardu masu yawa da ya kamata ya warware bayanai a kai. Ba mu ce ya sace kuɗin ba, amma ya kamata ya bayyana ina kuɗin suka dosa.”

Hukumar ta ƙara da cewa ba za ta yi musayar kalamai da kowa ba, saidai sakamakon binciken da za a fitar da shi ne bayan an kammala komai ake buƙata.

A nasa ɓangaren, Malami, ta bakin mai taimaka masa a harkokin yada labarai, Mohammed Doka – ya bayyana binciken a matsayin farautar siyasa, da ke cike da zarge-zarge marasa tushe.

A ranar 28 ga Nuwamba ne ya ofishin EFCC, inda ganawarsu ta kasance lafiya, yana mai tabbatar da cewa binciken zai wanke shi yayin da aka gano ainihin gaskiyar al’amarin.

By Babaji