
Wata Babbar Kotu da ke zaune a Maitama na Birnin Tarayya Abuja, ta amince da buƙatar Gwamnatin Tarayya, inda ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar da ta shigar akan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan zargin ɓata suna.
Alƙalin Kotu, Mai Shari’a Chizoba Orji, ya ɗage sauraron ƙarar, wadda ofishin Antoni Janar na Ƙasa ya shigar zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, domin cigaba da shari’ar.
A baya, Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Sanata Natasha ne bisa zargin yin furuci da ke ɓatanci da keta doka, wanda hakan ke zama cin mutunci ga wasu jami’ai ko hukumomi.
Masu sanya ido akan harkokin shari’a na kallon ƙarar a matsayin mai daukar hankali, duba da matsayin Sanatar da kuma yanayin siyasar jihar Kogi da kasa baki ɗaya.
Kotun ta bayyana cewa an dage ƙarar ne domin bada damar gudanar da shiri cikin kwanciyar hankali kafin a ɗora daga inda aka tsaya.
