Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sanar da cewa daga ranar 25 ga Fabrairu 2026 za ta daina manna alamar biza a cikin fasfo ga matafiya ’yan Nijeriya, inda za ta maye gurbinsa da cikakken tsarin visa na fasahar zamani, wato eVisa.
Hukumomi sun bayyana matakin a matsayin wani babban sauyi a tsarin shige da ficen ƙasar.
Sanarwar da Ofishin Bayar Da Biza Na Hukumar Shige Fice Ta Birtaniya (UKVI) ya fitar a Abuja ta ce duk sabbin bizar ziyara (Visit visas) da za a bai wa ’yan Nijeriya za su kasance na fasahar zamani ne kacokan. Wannan na nufin ba za a sake manna alamar biza a cikin fasfo ba; maimakon haka, masu neman biza za su riƙa duba matsayin shige da ficensu ta hanyar asusun su na UKVI a yanar gizo.
Hukumomin Birtaniya sun jaddada cewa tsarin neman biza bai canja ba. ’Yan Nijeriya za su ci gaba da cike fom na intanet, halartar cibiyar karɓar takardun biza domin yin rajistar bayanan yatsa (biometrics), tare da cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata. Abin da ya canja kawai shi ne yadda za a bayar da biza — daga takarda zuwa tsarin fasahar zamani.
An kuma fayyace cewa duk wanda ke da alamar biza a fasfo a halin yanzu ba zai fuskanci wata matsala ba. Bizar su za ta ci gaba da aiki har sai ta ƙare, kuma ba sai sun sauya ta ba saboda sabon tsarin.
Mataimakiyar Babbar Jakadiyar Birtaniya a Abuja, Gill Lever, ta ce manufar sauyin ita ce sauƙaƙa tafiye-tafiye tare da ƙara tsaro. A cewarta, “Canjin zuwa biza na dijital zai sauƙaƙa wasu muhimman matakai, ya ƙara tsaro, kuma ya rage dogaro da takardun biza.”
A cewar UKVI, sabon tsarin eVisa zai rage jinkirin aiki, domin ba za a riƙe fasfo na dogon lokaci domin manna biza ba. Haka kuma, matafiya za su iya duba ko raba bayanan bizar su a kowane lokaci daga ko’ina cikin duniya ta hanyar asusun su na yanar gizo.
Hukumomi sun ƙara da cewa, eVisa ba za ta iya ɓacewa, sata ko lalacewa kamar takardar biza ba, kuma za ta ba da damar tabbatar da matsayin shige da ficen mutum a ainihin lokaci (real-time verification). Bayan amincewa da visa, mai nema zai ƙirƙiro asusun UKVI kyauta domin samun damar shiga da amfani da eVisa cinsa.
Matakin na nuna sabon salo na zamani da Birtaniya ke ɗauka wajen tafiyar da iyakokinta, inda ’yan Nijeriya ke cikin rukuni na farko da za su fara cin gajiyar cikakken tsarin biza na dijital. Ga masu yawan tafiye-tafiye, dalibai da ’yan kasuwa, wannan sauyi zai zama wani muhimmin canji daga takardar biza zuwa cikakken rajistar shige da ficen dijital.
