Birtaniya ta yi watsi da batun biyan diyyar bautar da wasu ƙasashe

Spread the love

Biritaniya ta bayyana cewa ba za ta bijiro da batun biyan diyyar bautar da al’umma da ƙasar ta yi a wurin taron ƙungiyar ƙasashe Renon Ingila ta Commonwealth ba, wadda aka fara a Samoa ranar Litinin, amma ƙofa a buɗe take wajen tattaunawa da shugabannin da ke da buƙatar hakan.

Shugabanni da jami’ai daga ƙasashe 56 da Biritaniya ta yi wa mulkin mallaka ne ke halartar taron ƙungiyar ta Commaonwealth a wannan makon a ƙasar da ke tsibirin Pacific.

Gwamnatoci daban-daban da suka gabata a Biritaniya sun yi watsi da duk kiraye-kirayen da aka yi na biyan ƙasashen da ke buƙatar diyya amma Shugabar Hukumar Kula da Al’amuran Yankin Caribbean CARICOM, Hilary Beckles, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa da yiwuwar wannan matsaya ta sauya a ƙarkashin sabuwar gwamnatin jam’iyyar Labor bayan shekaru 14 na mulkin masu ra’ayin ƴan mazan jiya.

Sannan ana sa ran firaministan Burtaniya Keir Starmer da Sarki Charles za su halarci taron na Samoa, inda ake tunanin ɓullo da wannan buƙata a yayin da yake gudana.

Amma mai magana da yawun Starmer ya sake nanata cewa batun biyan diyyar baya cikin shirye-shiryen da za a duba a wurin taron na Commonwealth.

Duk da cewa batun biyan diyyar ba ya cikin ajandodin taron, mai magana da yawun na Starmer ya ƙara da cewa, za su ci gaba da duba lamuran da waɗanda abin ya shafa.

Sannan dukkanin waɗanda ke takararar kujerar sakatare janar na ƙungiyar ta Commonwealth sun nuna goyon bayansu akan ƙudurin na neman diyar bautarwar da aka yi wa magabata a ƙasashen da Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka. RFI 

By ukarofi