Blueprint ta rasa ɗaya daga cikin manyan ma’aikatanta

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Alhamis 29 ga watan Agusta, 2024 jaridar Blueprint ta rasa ɗaya daga cikin manyan ma’aikatanta, Mista John Oba bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Kafin rasuwarsa, Mista Oba shine shugaban ɓangaren ruwaito labaran noma na jaridar.

Wani daga cikin makusantansa ya ce da farko an kai shi babban asibitin da ke Wuse ne a Abuja inda ba a samu likitan da zai duba shi ba wanda daga nan ne aka kai shi asibitin Kings Care a ‘Wuse Zone 4’ inda yayin da aka isa, sai likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

A yayin da tawagar Blueprint ta je gaisuwar ta’aziyya zuwa gidan mamacin da ke Mpape, Manajan ɓangaren kula da harkokin ma’aikata, Malam Nuhu Sani, ya ce mamacin mutum ne mai nitsuwa tare da jajircewa da sadaukarwa ga aikinsa.

Ya kuma jajenta wa ahalin mamacin tare da fatan samun juriya daga gare su yayin alhinin rashin da aka yi mu su.

Cikin waɗanda suka halarci ta’aziyyar akwai Editan Blueprint, Mista Abdurrahman Abdurra’uf da Mataimakinsa, Mista Agi Onda da kuma Editan shirye-shirye Ahmid Lawal.

By Babaji