Daga UMAR GARBA a Katsina
A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na yaƙi da ta’addanci, gwamnatin jihar ta ƙaddamar da wani shirin fatatattakar ‘yan bindiga dake garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Shirin haɗin gwiwa ne tsakanin jami’an tsaro, gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Nasir Muazu ne ya sanar da hakan ga manema labarai, bayan wani taron majalisar tsaro ta jiha.
Gwamna Raɗɗa ne ya kira taron da nufin magance yawaitar hare-haren ‘yan bindiga waɗanda ke amfani da lokacin damina don aikin ta’addanci.
Kwamishinan ya ce, za a ci gaba da aikin samar da tsaro na tsawon kwanaki 30 a ƙananan hukumomi 19 da suka haɗa da Jibiya, Batsari, Safana, ɗanmusa, Kankiya, Faskari, ɗandume, Sabuwa, Dutsin-ma, Kurfi, ƙanƙara, Musawa, Matazu, Malumfashi, ɗanja, Bakori, Funtuwa, Charanchi da ɓatagarawa.
A cewar Dakta Nasir Mu’azu, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro baki ɗaya sun amince da baiwa ƙananan hukumomin da abin ya shafa ƙarfin gwiwa domin samar da hanyoyin gudanar da ayyukan tsaro, tare da jaddada hanyoyin tattara bayanan sirri daga al’umma.
“Waɗannan matakan na wakiltar cikakkiyar hanyar haɗin gwiwa don tinkarar ƙalubalen tsaro da ke fuskantar al’ummominmu. Gwamnatin jihar Katsina ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da jin daɗin duk mazauna jihar kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da waɗannan ƙudirori.
“Muna kira ga ɗaukacin ‘yan ƙasa da su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abin da ba a amince da shi ba,” inji shi.
