Boko Haram: ‘Yan Nijeriya 7,790 suka dawo bayan shafe shekaru 10 a Chadi

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin mutane 7,790 ne Gwamnatin Tarayya ta marabce su daga Jamhuriyar Chadi bayan shafe kusan shekaru goma a ƙasar a matsayin ƴan gudun hijira sakamakon yaƙin ƙungiyar Boko Haram.

Mai taimaka wa Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno kna harkar yaɗa labarai, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Gwamna Zulum shi ne wanda ya jagoranci tawagar wakilcin Gwamnatin Tarayya da rakiyar Ƙaramin Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci, Yusuf Sununu da Shugaban Hukumar kula da Ƴan gudun hijira da Waɗanda suka rasa matsuguni (NCFRMI), Aliyu Ahmed.

Ƴan gudun hijirar, waɗanda galibinsu ƴan Jihar Borno ne daga ƙauyukan da ke yankin Tafkin Chadi, sun samu kulawa daga Chadi sakamakon ta’addancin ƙungiyar da ya addabe su.

Gabannin dawo da mutanen na zangon farko, Gwamna Zulum ya wakilci Nijeriya wajen sanya hannu a yarjejeniyar ɓangarori uku da suka haɗa da gwamnatocin Nijeriya da ta Chadi da kuma Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Ƴan gudun hijira (UNHCR) a Baga Sola.

Ta ƙara da cewa, Gwmana Zulum ya jinjina wa Gwamnatin Chadi bisa yadda ta kula da dubunnan ƴan Nijeriya na tsawon shekaru.