Gwamnan Katsina zai gina katafaran bene mai hawa 20 a Legas

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarinsa na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya amince da gina katafaren Bene mai hawa ashirin a birnin Legas.

Jawabin ya fito ne daga bakin mai bai wa gwamnan shawara kan hulɗa tsakanin gwamnatoci, Hajiya Hadiza Mai Kuɗi bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa .

Ta ce ginin zai gudana ne a unguwar Kofi Abayomi da ke Victoria Island.

Hajiya Hadiza ta ce aikin ginin benen zai kasance mai ɗauke da gidaje talatin.

Ana sa ran nan da watanni 18 za a kammala aikin ginin wanda zai taimaka wa jihar wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga.

Jihar Katsina na fama da ƙarancin manyan kanfanoni da masana’antu da za su taimaka wa gwamnati wajen samun kuɗaɗen shiga.

Zaman majalisar shine na uku a cikin wannan shekarar 2025.