
A ranar Lahadi Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya ziyarci garin Ngoshe mai tazarar kilomita 40 daga Gwoza domin ganewa idonsa matakin ɓarnar da aka yi.
Zulum, wanda ya fara ziyarar kwana biyu na kwarin gwiwa da jajircewa ga wadanda harin Boko Haram ya rutsa da su a Ngoshe da Pulka, ya raba kudade da kayayyakin agaji ga sama da mutane 30,000 da lamarin ya shafa.
Da yake zantawa da manema labarai jim-kaɗan bayan ya duba al’ummar da abin ya shafa, gwamnan ya bayyana irin ɓarnar da aka yi a matsayin abin ban tsoro da ban tausayi.
Ya kuma tabbatar wa mazauna Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza cewa gwamnati za ta sake gina gidaje da ababen more rayuwa da aka lalata sakamakon hare-haren baya-bayan nan, tare da zafafa ayyukan tsaro na maido da dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Zulum ya ce ya umurci jami’an ma’aikatar sake gine-gine, gyara da sake tsugunar da jama’a da su gaggauta tantance irin barnar da aka yi da nufin gyara duk wasu gine-gine da suka ƙone.
Gwamnan ya bayyana cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta saki kudade ga rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa domin bunkasa ayyukan soji a yankin.
“Na yi farin cikin sanar da goyon baya da tallafin da gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta saki kwanan nan ga rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa kan ayyukan soji a wannan yanki baki daya,” inji gwamnan.




