Tsohon daraktan yaɗa labaran Ganduje ya koma ADC daga APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Darakta Janar na yaɗa labarai ga tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wato Salihu Tanko Yakasai, ya sanar da ficewarsa daga APC, inda ya koma jam’iyyar adawa ta ADC.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, Yakasai ya ce ya ɗauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da abokan siyasa, masu ruwa da tsaki, da kuma magoya bayansa.

Yakasai, wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamna a Kano a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar PRP, ya ce matakin da ya ɗauka na daga cikin dabarun sake tsara tafiyar siyasar sa domin cimma muradun al’umma.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan sauya sheƙa na iya sauya fasalin siyasa a Kano, musamman ganin irin tasirin da yake da shi a tsakanin matasa da magoya baya.

A shekarar 2022 ne Yakasai ya fice daga APC, inda ya koma PRP domin tsaya wa takara gwamna a zaɓen 2023. Daga bisani ya sake koma wa APC.

Wannan mataki na ƙara nuna yadda ‘yan siyasa suek tururuwar shiga ADC, wadda a kwanan nan sanatoci tara suka koma cikinta, lamarin da ke ƙara mata ƙarfi yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.

By Babaji