Yanzu-yanzu: Iran ta musanta batun tattaunawar sulhu da Amurka

Spread the love

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta musanta batun dukkan wata tattaunawa da Amurka, kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnati ta Tasnim ta rawaito a yau Litinin.

Iran ta yi wannan martani ne a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ya ce an yi “kyakkyawar tattaunawa mai anfani” tsakanin Washington da Tehran, wanda ya sa ya dakatar da shirin kai hari na wasu kwanaki.

Sai dai rahotanni na baya sun nuna cewa jami’an Iran sun daɗe suna musanta neman sulhu ko tattaunawa da Amurka, saboda a cewarsu, ba su ga dalilin yin hakan ba.

Haka kuma, wasu bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa duk da akwai wasu sakonnin da ake musayar su ta ɓoye, Iran a fili tana ƙin amincewa da tattaunawa a hukumance, lamarin da ke ƙara rikitar da gaskiyar abin da ke faruwa.

A halin yanzu, rikicin tsakanin ƙasashen biyu ya ƙara tsananta, inda ake fargabar cewa duk wata kuskure na iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin babbar yaƙi, musamman kan batun mashigin Hormuz da ke da muhimmanci ga man fetur na duniya.

Wannan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya ɗage shirin kai hari kan tashoshin wutar lantarkin Iran saboda fara tattaunawar sulhu da ƙasar.

By Babaji