Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Masaurautar Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin mai martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Ahmad Asha ta gudanar da bikin hawan sallah, a wani ɓangare na bukukuwan ƙaramar sallah a ranar Lahadi.
Bikin ya samu halartar manyan sarakunan jihar, jami’an gwamnatin jihar da jami’an tsaron soji, ‘yan sanda, NSCDC da sauran su.
Haka zalika bikin ya samu ƙayatarwa musamman hawan dawaki, ƙungiyar yan tauri, Fulani, ƙabilu mazauna garin Ƙaura Namoda da suka ƙunshi alummar Yarabawa, Inyamurai, Dakarkari, Buzaye da sauran su.
Da yake jawabin maraba da baƙi, Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha, ya bayyana cewa, bikin ya ƙunshi nuna al’adun masaurautar Ƙaura Namoda, tarihi da sauran muhimman al’amura da suka shafi masaurautar musamman al’adun alumma.
Basaraken yayi nuni da cewa bikin yana faɗakar da alummar masaurautar muhimman zumunta, zaman lafiya da haɗin kai.
Yayi kira ga al’ummar sa da su zauna lafiya lafiya da juna tare da yin addu’o’i don samun dauwamammen zaman lafiya a masaurautar, jiha da ƙasa baki ɗaya.
Alh. Muhammad Asha ya jinjinawa gwamnatin jihar ta Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewa da yayi wajen samar da filin jirgin ƙasa da ƙasa a babban birnin jihar. Yana mai nuni da cewa hakan zai bunƙasa tattalin arzikin Jihar ta kowane fanni.
“Ina yabawa Gwamna Dauda Lawal bisa sanar da filin jirgin ƙasa da ƙasa a Gusau, hakan zai kawo cigaba a jihar mu ta Zamfara tare da samar da ayyukan yi ga matasan mu masu yawa .” A cewar sa
Da yake jawabin sa, Gwamnan Jihar ta Zamfara, Dauda Lawal wanda shugaban ma’aikatan Jihar, Alh. Yakubu Mu’azu Haidara, ya jinjinawa masaurautar Ƙaura Namoda bisa gudanar da bikin hawan sallah.
Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewar gwamnatin sa zata cigaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da masaurautun gargajiya don samar da tsaro da cigaban alummar Jihar.
