Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya umurci dukkan membobin Majalisar Zartarwar Jihar da ke da niyyar tsayawa takarar muƙamai a babban zaɓen 2027 da su yi murabus daga muƙamansu.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin taron Majalisar Zartarwa karo na 64 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.
A cewar sanarwar da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, umarnin ya yi daidai da tanadin Dokar Zaɓe da kuma jadawalin zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
Sanarwar ta ce, “A yau, Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa na 64, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban Jihar Zamfara.”
A yayin taron, gwamnan ya umurci dukkan ‘yan majalisar zartarwa da ke sha’awar tsayawa takarar muƙaman siyasa da su yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
Haka kuma, gwamnan ya umurci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya fitar da sanarwa ga duk waɗanda aka naɗa a muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara, domin su sauka daga muƙamansu kafin wa’adin da aka gindaya.
Bugu da ƙari, an umurci Shugaban Ma’aikata da ya sanar da duk ma’aikatan gwamnati masu sha’awar tsayawa takara su bi wannan umarni.
Gwamna Lawal ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da yi wa al’ummar Jihar Zamfara hidima yadda ya kamata.


