Na shiga siyasa ne ba don na yi takara ba – Mannir Suleiman

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD, Katsina

Shugaban Gidauniyar Gwagware Musa Adamu Funtua, Kwamared Mannir Suleiman, ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne ba don ya tsaya takara ba.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Katsina.

A cewarsa, ya shiga siyasa ne domin ya taimaka wa Musa Adamu a ƙoƙarin da yake yi na ganin an sake zaɓen Malam Dikko Raɗɗa a matsayin gwamnan Jihar Katsina a karo na biyu.

Ya ƙara da cewa ya yanke wannan shawara ne sakamakon yadda Musa Adamu ya sadaukar da kansa wajen taimaka wa al’umma, musamman matasa, a yankinsa da ma jihar baki ɗaya.

Musa Adamu, wanda shi ne kwamishinan harkokin lafiya na Jihar Katsina, ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar a ƙarƙashin mulkin marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua.

Haka kuma, ya riƙe muƙamin kwamishina a ma’aikatu daban-daban a gwamnatin jihar tun a zamanin tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema.

Kwamared Suleiman ya ce muƙamai da Musa Adamu ya riƙa a gwamnatocin baya da na yanzu sun nuna irin ƙwarewa da kuma tsawon lokacin da ya ɗauka yana aikin siyasa wajen gina ƙasa da al’ummar yankin Funtua.

“Indai tafiyar Musa Adamu ce, zan ci gaba da ba da gudunmawa har sai an kai ga samun nasara,” inji Suleiman.

Ya kuma bayyana wasu ayyukan raya al’umma da gidauniyar ke aiwatarwa, waɗanda suka haɗa da tallafa wa marasa lafiya a wasu asibitocin jihar.

Hakazalika, gidauniyar ta ɗauki nauyin biyan kuɗin kula da yara fiye da dubu biyu da aka yi wa kaciya, tare da samar musu da kayan makaranta.

Kwamared Suleiman, wanda tsohon malamin kiwon lafiya ne, ya kuma taɓa shugabantar ƙungiyar malaman lafiya na tsawon lokaci.

By ukarofi