
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Yaƙi da Yaɗa Labaran Bogi CCC, ta nuna damuwa akan yadda labaran bogi ke zama haɗari acikin al’umma bisa yadda suka haifar da munanan fahimta game da rashin tsaro, siyasa da ruɗarwa a fannin yaɗa labarai a Nijeriya, tana mai gargaɗin hakan ya fara tasiri yayin da ake shirye-shiryen zaɓen 2027.
A sabon sadarwar zamani da sharhin lamuran al’umma da ta fitar, cibiyar ta bayyana yadda ake samun bambance-bambancen ra’ayoyi acikin al’umma da fahimta akan lamuran taɓarɓarewar harkokin tsaro da shugabanci.
CCC ta bayyana hakan a matsayin labarai masu ruɗarwa da ake yaɗawa da kafafen dijital da fagagen gargajiya kamar wuraren tarukan al’umma.
Daga cikin ababen da ake sauya tunanin al’umma a fili da kafafen sada zumunta akansu akwai al’amuran tsaro, ci-gaban siyasa, matsin tattalin arziƙi, fargabar harkokin addini da ƙabila, damuwa akan ‘yancin ɗan-adam, ruɗar da jama’a ta fuskar watsa labarai, maguɗin zaɓe, kalaman ɓatanci da alamun farko na rikici.
Ana ganin waɗannan ababen a matsayin makaman da ake amfani da su wajen gurɓata tunanin al’umma.
Ɗaya daga cikin misalan da CCC ta bayar akan wannan al’amari shi ne harin boma-boman ƙunar baƙin-waken da ya faru a Maiduguri kwanan nan, wanda ya yi daidai da lokacin tafiyar ziyarar aiki ta Shugaba Bola Tinubu zuwa Birtaniya, inda wasu suke ganin shugaban ya fifita lamuran ƙasar wajen akan ababen da ke faruwa a ƙasarsa duk da cewa ita ziyarar abu ne da ya shafi shugabancin Nijeriya ba raɗin kai ba.
