Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta sanar da cewa sun sami matsaya da mai horar wa ɗan asalin ƙasar Jamus Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin Super Eagles.
Sakataren hukumar Dakta Muhammed Sanusi shi ya bayar da wannan sanarwa a safiyar Talata.
Labbadia an haife shi a shekarar 1966, Fabarairu. Ya yi nasarar cin kofi biyu lokacin yana ɗan wasa a ƙungiyoyin Darmstadt 98, Hamburger SV, FC Kaiserslautern, Bayern Munich, FC Cologne, Werder Bremen, Armenia Bielefeld da Karlsruher SC.
A matsayin koci, ya jagoranci ƙungiyoyi irin su, VfL Wolfsburg, Hamburger SV da Bayer Leverkusen.
Ga yadda jadawalin Kocin Super Eagles su ka zamo daga shekarar 1949
John Finch (Ingila) – 1949
Daniel Anyiam (Nijeriya) – 1954-1956; 1964-1965
Les Courtier (Ingila) – 1956-1960
Moshe Beit Halevi (Israel) – 1960-1961
George Vardar (Hungary) – 1961-1963
Joey Blackwell (Ingila) – 1963 – 1964
József Ember (Hungary) – 1965-1968
Sabino Barinaga (Andalus) – 1968-1969
Peter ‘Eto’ Amaechina (Nijeriya) – 1969-1970
Karl-Heinz Marotzke (Jamus) – 1970-1971; 1974
Jorge Penna (Brazil) – 1972-1973
Jelisavčić ‘Father Tiko’ Tihomir (Yugoslavia) – 1974-1978
Otto Glória (Brazil) – 1979-1982
Gottlieb Göller (Jamus) – 1981
Adegboye Onigbinde (Nijeriya) – 1983-1984; 2002
Chris Udemezue (Nijeriya) – 1984-1986
Patrick Ekeji (Nijeriya) – 1985
Paul Hamilton (Nijeriya) – 1987; 1989
Manfred Höner (Jamus) – 1988-1989
Clemens Westerhof (Netherlands) – 1989-1994
Amodu Shaibu (Nijeriya) – 1994-1995; 1996-1997; 2001-2002; 2008-2010
Johannes Bonfrere (Netherlands) – 1995-1996; 1999-2001
Philippe Troussier (Faransa) – 1997
Monday Sinclair (Nijeriya) – 1997-1998
Bora Milutinović (Yugoslavia) – 1998
Thijs Libregts (Netherlands) – 1999
Christian Chukwu (Nijeriya) – 2002-2005
Augustine Eguavoen (Nijeriya) – 2005-2007; 2010; 2022
Berti Vogts (Jamus) – 2007-2008
Lars Lagerbäck (Sweden) – 2010
Samson Siasia (Nijeriya) – 2010-2011; 2016
Stephen Keshi (Nijeriya) – 2011-2014; 2015
Sunday Oliseh (Nijeriya) – 2015-2016
Gernot Rohr (Jamus) – 2016-2021
José Peseiro (Portugal) – 2022-2024
Finidi George (Nijeriya) – 2024
Bruno Labbadia (Jamus) – 2024-?
