Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata budurwa mai shekaru 25, Maimunatu Idris, ‘yar ƙaramar Hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa, ta amsa cewa ita ce ta kai wa saurayinta hari da wuƙa a wani otal da ke Jihar Kano, inda ta jikkata shi a mazaƙuta.
A cewarta, kishi ne ya sa ta aikata hakan bayan ta gano cewa saurayin nata na shirin auren wata mata, duk da cewa sun shafe shekaru shida suna soyayya.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce lamarin ya faru ne a Durbar Hotel da ke kan titin Ahmadu Bello Way, inda aka garzaya da saurayin zuwa Abubakar Imam Urology Hospital domin samun kulawar likitoci.
Da take bayyana wa ’yan sanda yadda lamarin ya faru, Maimunatu ta ce an taɓa sanya ranar aurensu, amma daga baya aka fasa. Ta ce har ta fasa auren wani mutum ne saboda saurayin ya hana ta, yana mai alƙawarin zai aure ta.
Sai dai, a cewarta, daga baya ta gano cewa saurayin ya shirya auren wata. Ta ƙara da cewa lokacin da ta je Kano domin halartar wani biki, ta samu damar ganawa da shi, kuma bayan ta saurari wasu saƙonnin murya a wayarsa da suka tayar mata da hankali, sai ta kai masa hari da wuƙa yayin da yake barci.
Matashiyar ta bayyana cewa yanzu tana nadamar abin da ta aikata.
Shi ma ɗan uwan saurayin ya ce iyayensu tun farko ba su amince da dangantakar tasu ba, yana mai kira ga hukumomi da su tabbatar an yi adalci a kan lamarin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma da zarar an kammala shi za a gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu bisa zargin yunƙurin kisa. Ya kuma tabbatar da cewa saurayin na ci gaba da samun kulawar likitoci.
