2027: Peter Obi ya gana da Obasanjo yayin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara ɗaukar zafi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya gana da tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a ranar Laraba, yayin da harkokin tuntubar juna da kulla alaƙar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 ke ci gaba da ƙara ƙarfi.

Mai ɗaukar hotunan yaƙin neman zaɓen Obi, Esther Umoh, ce ta bayyana hakan ta shafinta na ɗ (tsohon Twitter), inda ta wallafa hotunan ganawar tasu.

Sai dai ba ta bayyana inda aka yi taron ko kuma batutuwan da suka tattauna ba.

A cikin saƙon da ta wallafa, Umoh ta ce, “A yau da safe, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya gana da tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.”

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da manyan ‘yan siyasa ke ci gaba da gudanar da shawarwari da neman haɗin gwiwa domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Haka kuma, ganawar ta biyo bayan zargin da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi wa Obasanjo kwanaki kaɗan da suka gabata.

Atiku ya zargi Obasanjo da ƙirƙiro masa zarge-zarge domin taimaka wa wani ɗan uwansa ya samu galaba a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ko da yake Atiku bai ambaci sunan mutumin ba, ana ganin yana nufin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke neman wa’adi na biyu kuma ɗan asalin ƙabilar Yarbawa ne kamar Obasanjo.

A ranar 23 ga Janairu, Obasanjo ya yi zargin cewa Atiku ya bai wa marigayi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba, kuɗi har naira miliyan biyar domin ya jagoranci yunƙurin tsige shi daga mulki a wa’adinsa na farko.

Wannan zargi ya haddasa musayar kalamai tsakanin bangarorin biyu, inda kowannensu ke ƙaryata iƙirarin ɗayan.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin ganawar Peter Obi da Obasanjo za ta ƙara ɗaga hankalin jama’a, yayin da shirye-shiryen siyasa da ƙoƙarin ƙulla sabbin alaƙu ke ci gaba da ƙara armashi gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply