Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mai ba tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, shawara kan harkokin siyasa, Akin Osuntokun, ya bayyana cewa Obasanjo ne ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso domin ƙulla ƙawancen takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Osuntokun ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar ARISE News, inda ya musanta rahotannin da ke cewa Obasanjo na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
A cewarsa, idan akwai wata tikitin takara da Obasanjo ke mara wa baya, to ita ce ta Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso. Ya ce tsohon shugaban ƙasar shi ne ya jagoranci yunƙurin sasanta su tare da samar da damar tattaunawa tsakaninsu.
Ya ƙara da cewa babu wata hujja da ke nuna cewa Obasanjo na aiki a ɓoye domin amfanin Tinubu, yana mai cewa dukkan matsayinsa na siyasa ya nuna inda goyon bayansa yake.
Osuntokun ya bayyana cewa haɗin Obi da Kwankwaso na da ƙarfi kuma zai iya yin tasiri sosai a siyasar Nijeriya kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya kuma bayyana cewa tun kafin zaɓen 2023 an yi yunƙurin haɗa Obi da Kwankwaso, kuma da sun cimma matsaya a lokacin, da sun iya ƙulla yarjejeniyar raba wa’adin mulki tsakaninsu.
A ƙarshe, ya ce tikitin Obi da Kwankwaso ya fi ƙarfin wanda Jam’iyyar Labour ta fitar a zaɓen 2023, kuma zai iya zama ɗaya daga cikin manyan ƙawancen siyasa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
