Har yanzu akwai rashin isassun kuɗaɗe ga jami’an tsaro, duk da kasafin tsaro mai yawa – Irabor

Spread the love

Daga SANI SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Henry Lucky Irabor mai ritaya, ya bayyana cewa duk da yawan kuɗaɗen da ake ware wa fannin tsaro a kasafin kuɗin yasa, jami’an tsaro na ci gaba da fama da yarancin kuɗaɗen gudanar da aiki.

Irabor ya bayyana hakan ne yayin gabatar da muhimmin jawabi a taron tattaunawa kan tsaro da jaridar First Daily ta shirya domin cika shekara shida da kafuwa. Taken taron shi ne: “Ayyaana Dokar Ta-ɓaci Kan Tsaro: Daidaita Kalamai da Ayyuka.”

Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ayyana cikakken yaƙi da rashin tsaro, yana mai cewa lokaci ya yi da za a tattara dukkan ƙarfin gwamnati domin muryushe masu barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

A cewarsa, kashe kuɗin da Nijeriya ke yi a fannin soja bai kai kashi ɗaya cikin ɗari na Jimillar Arzikin ƙasa (GDP) ba, duk da cewa yasar na fuskantar manyan matsalolin tsaro.

Irabor ya kuma bayyana cewa fiye da kashi uku cikin huɗu na kasafin kuɗin tsaro na tafiya ne wajen biyan albashi da alawus-alawus na jami’ai, abin da ke rage kuɗin sayen kayan aiki, gyaransu da kuma zamanantar da rundunonin tsaro.

Ya ce, a kasafin shekarar 2025, rundunar sojin yasa ta samu amincewar kashe Naira biliyan 20.56 domin sayen kayan aiki, amma zuwa lokacin da yake magana, kashi 7.1 cikin 100 ne kacal aka fitar. Haka kuma rundunar sojin sama ta samu kasafin Naira biliyan 34.71 domin kula da jiragen yayi, amma kashi 13.9 cikin 100 ne kawai aka saki.

Tsohon shugaban tsaron ya jaddada cewa babbar matsalar da ke hana nasarar yayi da rashin tsaro ita ce rashin cikakken yudirin siyasa, yana mai cewa jarumtakar jami’an tsaro kaɗai ba za ta wadatar ba idan ba a samar da isasshen goyon baya daga gwamnati ba.

Shi ma tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mike Okiro mai ritaya, ya ce rashin isasshen tallafin gwamnati ga rundunar ’yan sanda a tsawon shekaru ne ya taimaka wajen taɓarɓarewar tsaro a yasar.

Okiro ya yi zargin cewa gwamnati ta raunana rundunar ’yan sanda duk da cewa ita ce ke jagorantar tsaron cikin gida. Ya kuma yi Allah-wadai da rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, yana mai cewa kowace hukuma na son ɗaukar yabo ita kaɗai idan an samu nasara a wani aiki.

Ya buyaci a inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin samun nasara a yayi da rashin tsaro a faɗin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply