Muna siyasa domin ci gaban al’umma, ba don son kai ba – Baffan Matasa

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Dan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Rano a yaryashin jam’iyyar NDC, Hon. Isa Ahmed Tijjani, wanda aka fi sani da Baffan Matasa, ya bayyana cewa babban dalilinsa na neman kujerar majalisa shi ne tabbatar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar mazaɓarsa, ba don biyan wata buƙata ta kansa ba.

Hon. Isa Ahmed Tijjani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a lokacin bikin yaye ɗaliban Makarantar Sakandaren ‘Yan Sanda da ke Dawakin Kudu.

Ya ce idan Allah Ya ba su nasara a zaɓen 2027, za su mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da shirye-shiryen da za su bunƙasa tattalin arzikin yankin Rano.

“Muna siyasa ne domin ci gaban al’umma. Burinmu shi ne tallafa wa matasa maza da mata su dogara da kansu, mu inganta ilimi, lafiya da noma, kasancewar noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin wannan yanki. Haka kuma za mu inganta harkokin sufuri domin bunyasa kasuwanci da tattalin arzikin al’umma,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su fito su karɓi katin zaɓensu yayin da ake gudanar da rajistar masu zaɓe, yana mai cewa katin zaɓe shi ne makamin sauyi da zai bai wa jama’a damar zaɓar shugabannin da za su kawo ci gaba.

Hon. Isa Ahmed Tijjani ya bayyana fatansa cewa jam’iyyar NDC za ta samu nasara a zaɓen shekarar 2027 domin aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply