Mun gaza tantance takardu kafin amincewa da hukumar bogi – Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Esther Walson-Jack, ta amince cewa ofishinta bai gudanar da cikakken bincike da tantance takardun da aka gabatar masa ba kafin ya amince da tsarin ma’aikata da kuma izinin ɗaukar ma’aikata na wata hukuma da ake zargin ta bogi ce mai suna Majalisar Shugaban ƙasa kan Bunƙasa Zuba Jarin ƙasashen Waje (PFIPC).

Walson-Jack ta bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da take ba da shaida a gaban Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai, wanda ke binciken rikicin da ya dabaibaye PFIPC da kuma ware mata kuɗaɗe har Naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Ta ce ofishinta ya amince da tsarin ma’aikatan hukumar da kuma ba ta izinin ɗaukar ma’aikata ne bayan an gabatar masa da abin da aka bayyana a matsayin dokar kafa hukumar, tare da takardar naɗin Adeniyi Adeyemi, wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne Darakta Janar na PFIPC.

“Ofishina ya karɓi takardar naɗi da kuma dokar kafa hukumar. Bisa waɗannan takardu da kuma tattaunawar da muka yi da wakilan PEAC/PFIPC ne muka amince da tsarin ma’aikata, sannan daga baya muka ba su izinin ɗaukar ma’aikata,” inji ta.

Sai dai ta amince cewa ya kamata ofishinta ya gudanar da ƙarin bincike kafin ya bayar da waɗannan amincewa, musamman ganin cewa daga baya an gano cewa duk takardun da aka gabatar masa jabun takardu ne.

Ta ce, “Yanzu da muka ga dukkan hujjoji da takardun da aka gabatar, mun yarda cewa ya kamata mu yi cikakken bincike da tantancewa kafin mu amince da tsarin ma’aikata da kuma izinin ɗaukar ma’aikata.”

Ta ƙara da cewa ofishinta ya san cewa PEAC ta taɓa wanzuwa a matsayin kwamitin wucin gadi, kuma takardun da aka gabatar sun haɗa sunayen PEAC/PFIPC, abin da ya sa aka ɗauki matakin amincewa.

“Duk da haka, da mun gudanar da cikakken bincike, da an gano ko waɗannan takardu na gaskiya ne ko a’a. Saboda haka, muna ɗaukar cikakken alhakin abin da ya faru, kuma za mu sake duba tsarin aikinmu domin ƙarfafa shi ta yadda ba za a sake samun irin wannan damfara ba,” inji ta.

Lamarin PFIPC ya kuma jawo hankalin Fadar Shugaban ƙasa, bayan da aka yi zargin cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya sanya hannu kan takardar naɗin Adeyemi.

Sai dai Gbajabiamila ya musanta zargin, yana mai cewa bai taɓa bayar da irin wannan takarda ba. Haka kuma, Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa takardar da ke ɗauke da sa hannunsa jabun takarda ce, tare da bayyana cewa tun da farko ya kai ƙorafi ga hukumomin tsaro kan batun.

A cewar rahotanni, jami’an Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya (IRT) sun kama Adeyemi a ranar 14 ga Yuli a Jihar Osun, yayin da bincike kan ayyukan wannan hukuma da ake takaddama a kanta ke ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply