Da ɗumi-ɗumi: Sanata Rufa’i Hanga ya fice daga NDC ya Koma APC

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sanatan Kano ta tsakiya Alhaji Rufa’i Sani Hanga, ya fice daga jam’iyyarsa ta NDC Kwankwasiyya, ya koma APC.

Hanga ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da Nasir Salisu Zango a yau Alhamis, inda yace ya ɗauki matakin ne bisa raɗin kansa da kuma nema wa kansa mutunci da kima a siyasance.

Wannan na zuwa ne tun bayan rasa takarar Sanatan da yake kai, da kuma aiwatar da wasu sauye- sauye a jam’iyyar ba tare da saninsa ba.

Ko a makon da ya gabata ne ma dai an hangi Sanata Hanga da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, lamarin da masu lura da al’amuran yau da kullum ke cewa da wuya bai koma ba.

By ukarofi

Leave a Reply