
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar ranar Alhamis ne tsohon Ministan Kuɗin Nijeriya kuma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu bayan shafe shekaru 87 a duniya.
Dikkon Sakkwato, Alhaji Ya’u Dogon Daji ne ya tabbatar da labarin, inda ya ce marigayin ya yi fama da rashin lafiya na kusan wata guda, kuma ana sa ran za a yi masa sallar jana’iza a Masallacin Sultan Bello na Sakkwato kafin a binne shi a Hubbaren Shehu a jihar.
Kafin rasuwarsa a wani asibitin Abuja, marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnatin Nijeriya a tsawon sama da shekaru 30 da ya shafe yana hidimta mata.
A shekarar 1988 ne ya riƙe muƙamin ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsare. Daga bisani ya zama Ministan Kuɗi tsakanin 1990 da 1991 a zamanin mulkin tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Haka kuma, ya taɓa zama babban jakadan Nijeriya a Birtaniya daga 1992 zuwa 1996, inda ya taimaka wajen zurfafa alaƙar difulomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Sardaunan ya kuma riƙe muƙamin babban sakatare a ma’aikatun kuɗi, kasuwanci, masana’antu da Tsare-tsaren ƙasa.
Marigayin ya bar mata, ‘ya’ya biyar, jikoki da sauran ‘yan uwa, ciki har da tsohuwar Karamar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya Aisha Abubakar.
