Hisbah ta haramta DJ da haɗa maza da mata a bukukuwa a Sakkwato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta sanar da haramta wasu al’adu da ake gudanarwa a bukukuwan aure da sauran tarukan jama’a, ciki har da amfani da DJ, bikin gabatar da kayan neman aure da aka fi sani da ‘Na Gani Ina So’, haɗa maza da mata wajen nishaɗi, da kuma yawan kashe kuɗi wajen kayan lefe, tana mai cewa waɗannan abubuwa ba su da tushe a koyarwar Musulunci.

Hukumar ta kuma hana amfani da waƙoƙin Wazigidi a bukukuwa, ɗaura lasifika a kan baburan adaidaita sahu (Keke Napep), zaman mata kusa da direbobin adaidaita sahu, salon aski da ta bayyana a matsayin marasa ɗa’a ga yara da matasa, da kuma almubazzaranci wajen sayen kayan lefe.

Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato, Malam Usman Abdullahi Jatau, ne ya bayyana sabbin matakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Sakkwato ranar Talata.

Ya ce manufar dokokin ita ce kare addini da kyawawan ɗabi’u na al’ummar jihar bisa koyarwar Musulunci.

A cewarsa, al’adar ‘Na Gani Ina So’, wadda ake gabatar da abubuwa kamar lemo, ruwan kwalba, biskit, alewa da goro ga iyalan amarya kafin aure, ba ta da wani asali a addinin Musulunci.

“Mun ayyana waɗannan sababbin al’adu (bid’a) da suka saɓa wa Sunnar Annabi Muhammad (SAW), kuma suna iya yin mummunan tasiri ga aure saboda sun kauce wa koyarwar Annabi,” inji Jatau.

Kwamandan Hisbah ya buƙaci masu shirin yin aure, iyayen amarya da ango da sauran ‘yan uwa su rungumi sauƙi wajen gudanar da bukukuwan aure, tare da gujewa al’adun da ke jefa iyalai cikin nauyin kuɗaɗe.

Ya ce, “Muna kira ga iyalan ango da amarya da kuma iyaye su ji tsoron Allah, su daina waɗannan ɗabi’u.”

Jatau ya kuma yi gargaɗin cewa Hukumar Hisbah za ta tabbatar da aiwatar da wannan umarni, tare da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu yana karya sabbin ƙa’idojin.

Ya ce wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe ga masu shirya irin waɗannan bukukuwa da kuma masu halarta, yana mai kira gare su da su ji tsoron Allah kafin a fara hukunta masu karya dokar.

Haka kuma ya shawarci masu shirin yin aure da su rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen kayan lefe, yana mai cewa bukukuwan aure masu tsada kan jefa sabbin ma’aurata cikin bashi da matsin tattalin arziki tun farkon rayuwar aurensu.

By ukarofi