Ayyukan raya ƙasa a Arewa: Tinubu na cika alƙawari

Spread the love

A cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da manyan shirye-shiryen raya ƙasa da suka shafi sassa daban-daban na Nijeriya, musamman fannin tsaro, ababen more rayuwa, noma, ilimi da makamashi. Arewacin ƙasar na daga cikin yankunan da ake aiwatar da wasu daga cikin waɗannan ayyuka.

A fannin tsaro, gwamnati ta amince da ƙirƙirar sabbin Rukunonin Sojoji (Divisions), tare da sake tsara yankunan aiki domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka. Haka kuma an amince da ƙarin kayan aiki da gina sabbin barikoki domin inganta ayyukan jami’an tsaro.

A ɓangaren hanyoyi, Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka irin su hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, da wasu hanyoyi a jihohin Borno, Adamawa, Katsina, Sakkwato, Kebbi da sauran jihohin Arewa. Waɗannan ayyuka na da muhimmanci wajen bunƙasa kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma.

A fannin noma, gwamnati ta bayyana shirye-shiryen tallafa wa manoma da bunƙasa samar da abinci, yayin da a ɓangaren makamashi ake ƙarfafa tace mai a cikin gida da samar da kayayyakin hasken rana domin rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.

Haka kuma, shirin Asusun Lamunin Ilimi (NELFUND) ya bai wa dubban ɗalibai damar ci gaba da karatu ba tare da tsadar kuɗin makaranta ta zama cikas ba.

Sai dai duk da waɗannan matakai, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da damun sassan Arewa, musamman hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da hare-haren da ake kai wa manoma. Haka kuma al’umma na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa da hauhawar farashi.

Saboda haka, lokaci ya yi da gwamnati za ta tabbatar cewa ayyukan da aka ƙaddamar sun kai ga sakamakon da talakawa za su gani a zahiri. Ayyukan raya ƙasa ba su cika manufarsu ba sai lokacin da suka inganta rayuwar jama’a, suka samar da tsaro mai ɗorewa, suka buɗe damar ayyukan yi tare da rage talauci.

Jaridar Blueprint Manhaja na ganin cewa ci gaba mai ɗorewa yana buƙatar haɗin kan gwamnati, hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da kuma ‘yan ƙasa. Haka kuma, gwamnati ta ci gaba da sauraron koke-koken jama’a tare da hanzarta kammala ayyukan da aka fara.

Idan aka ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi yadda ya kamata, tare da aarfafa gaskiya, riƙon amana da sa ido kan ayyukan gwamnati, akwai damar da Arewa da Nijeriya baki ɗaya za su samu ci gaba mai amfani ga kowa.

By ukarofi

Leave a Reply