Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin jaridun Blueprint da Mahana ya zaɓi Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin Gwarzon Shekara ta 2025 bisa irin jagorancinsa, gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da kuma ƙoƙarinsa na ƙarfafa cibiyoyin siyasa a Nijeriya.
Lambar yabon, wadda ita ce mafi girma da kamfanin ke bayarwa a duk shekara, na karrama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa ta fuskar shugabanci, hidimar jama’a da kuma ayyukan raya ƙasa a shekarar da ake dubawa.
Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Jaridun Blueprint, Salisu Umar, ya ce an zaɓi Farfesa Yilwatda ne bayan cikakken nazari da aka gudanar kan masu riƙe da muƙaman gwamnati, shugabannin siyasa da sauran fitattun ’yan Nijeriya da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban siyasa, tattalin arziki da zamantakewar ƙasa.
Ya ce, lambar yabon ta nuna amincewa da irin jagorancin da Yilwatda ya nuna tun bayan hawansa kujerar Shugaban APC a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
A cewarsa, tun bayan da ya karɓi ragamar jam’iyyar, Yilwatda ya rungumi salon shugabanci na haɗin kai da cimma sakamako, inda ya mayar da hankali wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyar, inganta haɗin kan mambobinta da kuma ba da shugabanci mai inganci ga dukkan sassan APC.
Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, APC ta ci gaba da ƙarfafa matsayinta a matsayin jam’iyya mai mulki ta hanyar inganta daidaito a cikin gida, faɗaɗa tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar a faɗin ƙasar nan.
Salisu Umar ya kuma yaba wa Yilwatda bisa abin da ya kira mutunci, ƙwarewa da jajircewa wajen yi wa ƙasa hidima, yana mai cewa ya haɗa ilimin jami’a, gogewar aiki da kuma ƙwarewar siyasa wajen inganta tsarin dimokuraɗiyya.
Haka kuma, ya ce an karrama shi ne saboda ƙoƙarinsa na sasanta rikice-rikice cikin lumana, gina yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma aiwatar da sauye-sauyen da suka ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a cikin APC tare da ƙara wa jama’a amincewa da tsarin siyasar ƙasar.
Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda ƙwararren malami ne, injiniya, masani a harkokin fasahar sadarwa, jami’in gwamnati kuma ɗan siyasa.
An haife shi ranar 8 ga Agustan 1968 a garin Dungung da ke ƙaramar Hukumar Kanke a Jihar Filato. Ya yi karatun sakandare a Boys’ Secondary School, Gindiri, kafin ya samu digirin farko a Jami’ar Tarayya ta Aikin Noma da ke Makurdi, sannan ya yi digirin digirgir a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, kafin daga bisani ya samu digirin digirgir na uku (PhD) a fannin Injiniyan Lantarki da Kwamfuta daga Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka.
Ya kwashe sama da shekara 26 yana aiki a Jami’ar Tarayya ta Aikin Noma da ke Makurdi, inda ya kasance Daraktan Cibiyar Fasahar Sadarwa (ICT) na farko, kuma ya jagoranci sauye-sauyen fasaha da suka inganta ayyukan gudanarwa da na ilimi a jami’ar.
Saboda ƙwazonsa, jami’ar ta karrama shi da lambobin yabo na Mafi Kyawun Ma’aikaci da kuma Mafi Kyawun Darakta.
A matsayinsa na masani a fannin ICT, ya yi aiki tare da ƙungiyoyi na duniya da suka haɗa da Tarayyar Turai (EU), UNICEF, Bankin Duniya (World Bank) da TECHɓILE USA, inda ya jagoranci ayyukan da suka shafi amfani da fasaha wajen inganta shugabanci da ayyukan gwamnati.
A shekarar 2017, an naɗa shi Kwamishinan Zaɓe na Hukumar Zaɓe ta ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC), inda ya taka rawa wajen sauye-sauyen tsarin zaɓe, amfani da fasaha a zaɓe da kuma faɗaɗa damar kaɗa ƙuri’a ga ’yan gudun hijira na cikin gida (IDP) da masu buƙata ta musamman (PWD).
Ya yi murabus daga INEC a shekarar 2021 domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Filato a ƙarƙashin inuwar APC, sannan ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a jihar yayin babban zaɓen shekarar 2023.
Daga bisani ya zama Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, inda ya mayar da hankali kan inganta gaskiya, amfani da bayanai wajen yanke hukunci da kuma ƙarfafa shirye-shiryen jinƙai da kariyar zamantakewa.
Haka kuma, ya kasance mamba a Kwamitin Shugaban ƙasa Kan Gudanar da Tattalin Arziki, sannan ya jagoranci Tattaunawar Turai da Afirka Kan Hijira da Ci Gaba, inda ya ba da gudummawa wajen tsara manufofi a matakin ƙasa da na duniya.
