Amurka za ta dakatar da ayyukan bada biza a Abuja daga watan Agusta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa daga ranar 1 ga Agustan 2026, za ta dakatar da ayyukan karɓa da sarrafa buƙatun bizar yau da kullum a Ofishin Jakadancinta da ke Abuja, tare da wasu ofisoshin jakadanci guda 24 da ke faɗin nahiyar Afirka.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, matakin na daga cikin wani sabon shiri na sake fasalin ayyukan ofisoshin jakadancinta a ƙasashen waje, domin tattara ayyukan sarrafa biza a wasu cibiyoyi na yankuna. Hakan, a cewarta, zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, rage kuɗaɗen gudanarwa, tare da tabbatar da daidaito wajen tantance masu neman biza da yanke hukunci kan buƙatunsu.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce wannan sauyi ya yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, na fifita tsaro da muradun ƙasar.

Sanarwar ta ce, “Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na ci gaba da nazarin yadda take gudanar da ayyukanta a ƙasashen waje domin tabbatar da cewa suna tafiya cikin inganci tare da kare muradun Amurka. Wannan ya haɗa da tsarin ba da biza wanda ke tabbatar da tsauraran matakan bincike da tantance masu neman biza.”

Ma’aikatar ta jaddada cewa, duk da wannan sauyi, ofisoshin jakadancin da abin ya shafa za su ci gaba da gudanar da sauran ayyukan konsula da na diflomasiyya kamar yadda aka saba, kuma ba za a rufe su ba.

Baya ga Abuja, sauran biranen da za a dakatar da ayyukan ba da bizar yau da kullum sun haɗa da Asmara, Bamako, Banjul, Brazzaɓille, Bujumbura, Conakry, Cotonou, Durban, Freetown, Gaborone, Harare, Juba, Libreɓille, Lilongwe, Lusaka, Maputo, Maseru, Mbabane, N’Djamena, Niamey, Nouakchott, Ouagadougou da Windhoek.

Sai dai ma’aikatar ta bayyana cewa wannan sabon tsari ya shafi buƙatun bizar yau da kullum kawai, ba ya shafar sauran ayyukan jakadanci ko konsuloshi.

Haka kuma, ta tabbatar da cewa bizar da aka riga aka bayar ba za ta rasa ingancinta ba, kuma masu ita za su ci gaba da amfani da ita bisa ƙa’ida.

A ƙarƙashin sabon tsarin, masu neman biza daga ƙasashen da abin ya shafa za su riƙa gabatar da buƙatunsu ta hanyar wasu cibiyoyin sarrafa biza na yankuna da Amurka za ta ayyana, yayin da ofisoshin jakadanci da konsuloshi za su ci gaba da ba da sauran ayyukan diflomasiyya da na konsula.

By ukarofi

Leave a Reply