Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Makarantar Police Secondary School (PSS) da ke Dawakin Kudu a Jihar Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai 184 da suka kammala karatunsu, wanda shi ne karo na farko tun bayan kafuwar makarantar a shekarar 2023.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamandan makarantar, SP Mukhtar Haruna Hadeja, ya bayyana cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Mustapha Bala Dawaki, ne ya samar da makarantar tare da miya ta ga Gwamnatin Tarayya da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
SP Hadeja ya bayyana farin cikinsa da samun damar jagorantar makarantar a matsayin kwamanda na farko da kuma shaidar yaye ɗalibai 184 a karon farko.
Ya taya ɗaliban murnar kammala karatunsu tare da shawarce su da su kasance jakadun kirki na makarantar a duk inda suka samu kansu.
“Ina kira gare ku da ku kasance masu hayuri, gaskiya da riƙon amana. Ku yi amfani da ilimin da aka koya muku domin gina kanku da kuma yi wa ƙasa hidima,” inji shi.
Kwamandan ya kuma yaba wa ɗimbin mutane da yungiyoyi da suka ba makarantar gudunmawa wajen bunƙasa ayyukanta.
Ya bayyana cewa Shugaban AA Rano, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, yana ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 154 tun daga fara karatunsu har zuwa kammalawa, tare da kula da harkokinsu lokacin hutun makaranta.
Haka kuma ya ce AA Rano ya gina babban masallaci mai ɗaukar mutane kusan 600, tare da makarantar Islamiyya, ajijuwa huɗu, ofisoshin malamai da kuma banɗakuna.
SP Hadeja ya kuma yabawa Alhaji Mustapha Ado Mai Amasco bisa gina katangar da ta kewaye dakunan kwanan ɗalibai mai tsawon mita 372, tare da gode wa Dr. Kabiru Ibrahim na Kainuwa Clinic saboda tallafin magunguna da yake bai wa makarantar.
Ya kuma jinjina wa Hon. Mustapha Bala Dawaki bisa rawar da ya taka wajen samar da makarantar, yana mai cewa wannan na daga cikin manyan ayyukan ci gaban da ya kawo wa mazaɓarsa.
A nasa jawabin, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya, AIG Ahmed Garba, ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.
Ya buƙaci al’umma su ci gaba da tallafa wa makarantar, tare da taya ɗaliban murnar kammala karatunsu da yi musu fatan samun nasara a rayuwa.
AIG Ahmed Garba ya kuma yaba wa AA Rano, Alhaji Mustapha Ado Mai Amasco, Dr. Kabiru Ibrahim Kainuwa, Alhaji Aminu Dawaki da sauran masu hannu da shuni bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunyasa makarantar.
Ya shawarci ɗaliban da aka yaye da su kasance jakadu nagari na makarantar ta hanyar nuna ɗa’a, gaskiya, sadaukarwa, hangen nesa da kuma girmama al’umma.
Shi ma Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umar (Autan Bawo), ya yi kira ga ɗaliban da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen taimakawa ƙasa, musamman a fannin yaƙi da matsalar tsaro.
Ya kuma yaba wa masu hannu da shuni da ke tallafa wa marasa ƙarfi wajen samun ilimi, tare da kira ga sauran masu hali da su kwaikwayi wannan kyakkyawan aiki.
Bikin ya samu halartar Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya mai kula da Shiyya ta ɗaya, AIG Ahmed Garba; Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori wanda wakilinsa ya halarta; jami’an Rundunar ‘Yan Sanda; wakilan sarakunan gargajiya; shugabannin ƙananan hukumomi; iyaye; malamai da sauran manyan baƙi.
An gudanar da bikin ne a filin faretin makarantar da ke Dawakin Kudu, inda aka karrama ɗaliban da suka kammala karatunsu tare da yabawa waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban makarantar.
