Tinubu ya umarci jami’an tsaro su farauto maharan da suka kashe mutum 30 a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 30, tare da umartar jami’an tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Harin, wanda ya faru da safiyar ranar Litinin, ya jawo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na cikin gida da na ƙasashen waje, yayin da har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana harin a matsayin mummunan ta’addanci da aka kai kan fararen hula ba tare da wani dalili ba.

Shugaban ƙasar ya ce ya umarci rundunar sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da na leƙen asiri su yara zage damtse wajen gudanar da ayyuka a yankunan da abin ya shafa domin gano masu hannu a harin, kama su tare da tabbatar sun fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Tinubu ya bayyana cewa waɗanda ke ƙoƙarin tarwatsa zaman lafiyar da aka fara samu a Jihar Kaduna ba za su tsira daga hukuncin gwamnati ba.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin Gwamna Uba Sani, da kuma ɗaukacin al’ummar jihar bisa wannan babban rashi.

Shugaban ƙasar ya sake jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa hukumomin tsaro ta hanyar samar musu da kayan aiki, bayanan sirri da sauran abubuwan da suke buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Haka kuma ya yi kira ga al’ummomin yankunan da abin ya shafa da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri, yana mai cewa haɗin kan jama’a da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen daƙile hare-hare da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply