Nijeriya na da gangar iskar gas sama da tiriliyan 200 a rumbun ajiyarta, inji Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya ta mallaki sama da ganga tiriliyan 200 na albarkatun iskar gas a majiyarta, lamarin da ya sa ta shiga sahun ƙasashe masu mafi yawan arziƙin a Nahiyar Afirka.

Ministan ya faɗi haka ne a ranar Alhamis a yayin taron Ƙungiyar Ci-gaban Kasuwancin AKK ta Jihar Neja (Niger State AKK Business Development Forum), wanda aka gudanar a Minna.

Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya a yanzu tana iya fitarwa domin ciyar da masana’antu gaba, samar da makamashi, samar da ayyukan yi da kuma nasarori a fannonin ƙasa da dama a ƙoƙarinta na bunƙasa lamuran ƙasa da al’umma.

Mohammed Idris, wanda ya samu wakilcin Darakta-Janar na gidan yaɗa labarai na Voice of Nigeria (VON), Alhaji Jibrin Ndace, ya bayyana cewa bututun AKK na bin tsarin shirin Sabunta Fata na Shugaban ƙasa saboda yana samar da abin da ake buƙata wajen kai gas kai-tsaye ga masana’antu, tashoshin lantarki da kasuwanci, yana mai cewa wannan zai rage adadin kuɗaɗe da ake kashewa wajen gudanar da harkokin kasuwanci, inganta gogayya da kuma faɗaɗa damarmakin tattali ga miliyoyin ‘yan Nijeriya.

A cewar ministan, a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, gwamnatin tarayya na aiwatar da kyawawan sauye-sauye da nufin sake farfaɗo da harkokin fannoni da dama a Nijeriya da mayar da ita babbar cibiyar zuba jari a Afirka.

Haka kuma, ya zayyano wasu daga cikin sauye-sauyen da ke samar da sakamakon da ake buƙata da suka haɗa da cire takunkumin tsare-tsare na tsawon lokaci domin inganta harkokin tattali, gyare-gyare masu ma’ana a fannin mai da gas domin bunƙasa zuba jari da samar da motoci masu amfani da iskar gas na shirin shugaban ƙasa (CNG), wanda ya taimaka wajen samar da sufuri mai sauƙi ga al’umma.

Har ila yau, Ministan ya ce gwamnatin tarayyar za ta cigaba da zuba muhimman ayyukan raya ƙasa, waɗanda suka haɗa da titina, layin dogo, tashoshin lantarki da sadarwar dijital, yana mai cewa matakin ya taimaka wajen haɓaka fannoni da dama a Nijeriya.

By Babaji