Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Wakilin Manajan Kamfanin Felicity Solar, Auwalu Sidi Muhammad Tankwai, ya bayyana cewa kamfanin ya horar da matasa sama da 100 sana’o’in da suka shafi amfani da fasahar hasken rana (Solar) kyauta, domin samar musu da hanyar dogaro da kai da bunƙasa tattalin arzikinsu.
Tankwai ya ce manufar kamfanin ita ce rage rashin aikin yi a tsakanin matasa tare da ba su ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai da kuma tallafa wa iyalansu da al’ummarsu.
Ya bayyana cewa samar wa matasa ayyukan yi na daga cikin hanyoyin magance matsalolin tsaro tun daga tushe, domin idan matasa sun samu abin yi, hakan zai rage zaman banza da aikata laifuka.
A cewarsa, wannan wata gudummawa ce da kamfanin ke bayarwa ga al’umma da gwamnatin jihar domin rage nauyin da ke kan gwamnati wajen samar da ayyukan yi.
Tankwai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙara haɗin gwiwa da cibiyoyin horas da matasa irin wannan domin bunƙasa sana’o’in zamani da al’umma ke buƙata, musamman a birane da yankunan karkara.
Ya ce sana’ar amfani da makamashin hasken rana ta samu karɓuwa sosai a Nijeriya, kuma tana da damar samar da dubban guraben ayyukan yi idan aka ba ta kulawar da ta dace.
Da yake bayyana tarihin kamfanin, Tankwai ya ce Felicity Solar ya fara ne da ma’aikata kaɗan, amma a yau ya bunƙasa zuwa matakin da yake ɗaukar matasa da dama aiki.
Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri fasahar amfani da hasken rana ne domin taimaka wa talakawa da mazauna karkara su samu wutar lantarki cikin sauƙi, amma a halin yanzu tsadar kayan aikin ta sa mutane da dama ba sa iya cin gajiyar fasahar.
A cewarsa, a yau ana buƙatar kuɗi masu yawa domin samar da tsarin hasken rana ko da na ƙaramin gida ne, lamarin da ya sa talakawa da mazauna karkara ke fuskantar ƙalubale wajen mallakar irin waɗannan kayayyaki.
Saboda haka, ya buƙaci gwamnati ta samar da hanyoyin da za su rage farashin kayayyakin hasken rana, ta yadda talakawa da mazauna karkara za su samu damar amfani da su kamar yadda aka tsara lokacin da aka ƙirƙiri wannan fasaha.
