Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata ‘yar yarinya yar gudun hijira Amina Suleiman yar shekara 18 da haihuwa a ƙauyen Ɗanmarke daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta gudu bayan da yan’uwanta suka yi ƙoƙarin tilasta mata ta auri wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Babaye da ke zaune a unguwar Mai Zare.
Wani jami’in tsaro na JTF ya ƙarƙashin kwamanda Abba Sarki na shiyar Funtua ya gabartar da yarinyar tare da yi mata tambayoyi.
Jami’in ya bayyana cewa yarinyar ta gudu daga ƙauyen su bayan da ‘yan uwan iyayen da take zaune da su suka ka yi ƙoƙarin tilasta mata ta auri wani ƙasurgumin ɗan bindiga a ƙauyen.
Iyayen ta sun daɗe da rasuwa amma tana zaune wajen yan’uwanta amma suka nace sai ta auri ɗan bindigan, har ansa ranar biki tare da biyan sadaki,”Inji jami’in JTF.
Yace Amina ta isa tashar mota na garin Ɗanmusa ba tare da ta san inda take ba ko inda za ta sai da wasu mutane suka taimaka ganin halin da take ciki suka ɗauke ta zuwa wajen su a nan Funtua.
A wani faifan bidiyo da hukumar tsaro ta JTF suka fitar bayan sun yi fira da ita a garin Funtua, Amina tace ta gudu ne bisa ƙoƙarin tilasta mata da mai riƙon ta suka yi na aurar da ita ga wani ƙasurgumin ɗan bindiga a ƙauyen wanda tace ita kuma gara ta rasa ranta da ta aure sa.
“A karon farko da muka haɗu yace yana so na amma ni bana son sa sai ya kwaɗa mani wani ƙarfe a kafaɗar hannu na da yar yanzu yana mani ciwo,”Inji Amina.
Amina ta faɗa cewa duk da rashin amincewa da ta aure sa , yan uwan nata suka umurce ta da dole ta koma wajen sa ta faɗa masa ba za ta aure sa ba.
“Yan Uwan nawa sun umarce ni da inje in faɗa masa ba zan aure sa ba duk da sun san idan na faɗa masa haka kashe ni zaiyi, ni kuma gara na mutu da in aure shi,”Inji Amina.
Da aka tambaye ta ko za ta koma ƙauyen da ta fito sai tace “ba zata koma ba ta gwammace ta zauna ita kaɗai har ta sami mai taimaka mata da a tilasta mata ta auri ɗan bindiga,”tace.
“Gara in zauna a nan ni kaɗai da in auri wanda bai da wata sana’a sai ta kashe mutane,”a cewar Amina.
Barazana da ɗan bindigan ya yi na bankawa ƙauyen wuta idan ba a aurar masa da Amina ba ya nuna halin fargaba da zullumi da alummomi da ke zaune a irin waɗannan yanki suke faɗawa.
Wannan lamari na nuna damuwa da zullumi da irin waɗannan yan mata ke fadawa da amfani da matsi da barazana ga rayuka wajen tilasta buƙatar su ga al’umma.
