Daga UMAR GARBA a Katsina
Albarkacin zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu wato kakakin tsohon shugaban ƙasar, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya da riƙon amana gami da tausayin talakawa.
Garba Shehu, ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a duniya.
“Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci.” Inji kakakin.
Garba Shehu ya ƙara da cewa siyasa da cin hanci da rashawa suna tafiya kafaɗa da kafaɗa a ƙasashe da dama, ciki har da Nijeriya.
“Tunanin mutane shi ne duk ɗan siyasa ɗan rashawa ne. Amma shi sunansa “Mai gaskiya” saboda gaskiyarsa da rashin ɗaukar duniya da zafi.”
Garba Shehu ya ƙara da cewa Buhari ya yi kamfe ne kan inganta tattalin arziƙi da samar da tsaro da yaƙi da rashawa.
“A zamanin mulkinsa, ƙasar ta ga yadda aka ɗauki matakai masu yawa domin yaƙi da talauci. Buhari ya mayar da hankali kan inganta kiwon lafiya, inda a zamaninsa aka cire ƙasar daga cikin masu fama da cutar polio,” Inji kakakin tsohon shugaban ƙasar.
