NIMET ta yi hasashen samuwar ƙura da hazo na kwana uku daga Laraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar kula da Yanayi, NIMET ta yi hasashen samun ƙura da hazo daga ranar Laraba zuwa Juma’a a Nijeriya.

Hasashen da hukumar ta yi a ranar Talata ya nuna cewa za a samu matsakaicin hazo da ƙura a ranar Laraba na tsawon hangen kilomita 2 zuwa 5 a arewacin Nijeriya.

Haka ma a yankin Arewa ta Tsakiya da kudanci, inda ta ce za a samu hazo sakamakon matakin yanayin sanyi musamman a yankuna masu koguna.

NIMET ta yi kira ga al’umma da su ɗauki matakan kariya daga ƙurar wadda ka iya haddasa yaɗuwar cutuka musamman masu tarin fuka da waɗanda ke da alaƙa da numfashi.

Ta kuma nemi da su kasance cikin masu sauraron samun sabbin rahotanninta.

By Babaji